- Shugaba Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kubutar da sauran dalibai mata na jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara
- Bada umarnin ya biyo bayan sace daliban jami’ar tarayya da aka yi
- Tuni dai sojoji suka ceto 6 daga cikin daliban da aka sace bayan faruwar lamarin
Shugaba Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kubutar da sauran dalibai mata na jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara, wadanda ‘yan ta’adda suka sace kwanan nan.
Kimanin dalibai 24 ne rahotanni suka ce an yi garkuwa da su bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Sabon-Gida da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara da sanyin safiyar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Rashin Biyan Tara Ya Sanya Tsare Fursunoni 4k a Gidajen Yari – Ministan Tinubu
Jami’in yada labarai na rundunar Operation Hadarin-Daji, Kyaftin Ibrahim Yahaya, ya tabbatar da cewa sojoji sun ceto shida daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su.
Shugaba Tinubu, ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika a matsayin wani abin zargi na sace-sacen mutane, yana mai cewa babu wani dalili na ɗabi’a ga irin wannan munanan laifukan da ake yi wa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, wanda “laifin su” kawai shi ne neman ilimi mai inganci.
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan (kafofin yada labarai da wayar da kan jama’a) Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Lahadi, yayin da shugaban ke jajanta wa dukkan iyalan da wannan abin bakin ciki ya shafa kai tsaye, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da hakki mai nauyi na kare duk wani dan kasar Najeriya.
A bisa wannan alkawari, Tinubu ya tabbatar wa iyalan daliban da aka sace cewa ana duk wani kokari wajen ganin sun dawo lafiya.
Shugaban ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi sun kasance wuraren ilimi, ci gaba, da damammaki, kuma sun kubuta daga munanan ayyukan ta’addanci.
A wani labarin kuma, Jihar Jigawa Ta Samu Mutane 91 da Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar Mashako
Jihar Jigawa ta samu mutane 91 da ake zargin sun kamu da cutar mashako a kananan hukumomi 14
An samu bullar cutar mashako a sassan arewacin Najeriya a cikin watanni hudu da suka gabata
Wannan na faruwa ne musamman a wasu jihohi 4 da ke makwabtaka da ita
Jihar Jigawa ta samu mutane 91 da ake zargin sun kamu da cutar mashako a kananan hukumomi 14.
Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta Jigawa Dr Salisu Muazu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar a ranar Asabar.