Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC a ranar Talata ta fitar da jadawalin gudanar da zabukan gwamnonin jihohin Edo da Ondo
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC a ranar Talata ta fitar da jadawalin gudanar da zabukan gwamnonin jihohin Edo da Ondo, Tribune Online ta rawaito.
A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun Sam Olumekun, Kwamishinan zabe kuma Shugaban Kwamitin Watsa Labarai da Ilimin Masu Zabe, Za a gudanar da zaben Gwamnan Edo a ranar Asabar 21 ga watan Satumba 2024 yayin da za a gudanar da irin wannan zaben a jihar Ondo a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba 2024.
KARANTA WANNAN: Akpabio Ya Nemi Hadin Kai Tsakanin ‘Yan Majalisa Don Tunkarar Kalubalen Najeriya
Da yake karin haske kan tsarin da zai tunkari zaben, Kwamishinan INEC na kasa ya bayyana cewa a zaben Edo, “Za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyya daga ranar 1 zuwa 24 ga watan Fabrairun 2024.
Sannan kuma INEC tace za a fara gabatar da jerin sunayen ‘yan takarar ta hanyar yanar gizo daga 9.00 na safiyar ranar 4 ga watan Maris 2024 kuma rufewar zata kasance da karfe 6.00 na yamma ranar 24 ga watan Maris 2024.”
Har ila yau, gabanin zaben gwamnan Ondo, “Za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu daga ranakun 6 zuwa 27 ga watan Afrilu, yayin da za a fara gabatar da jerin sunayen ‘yan takarar ta hanyar yanar gizo da karfe 9.00 na safiyar ranar 29 ga watan Afrilu 2024 wanda kuma za a rufe da karfe 6.00 na yammacin ranar 20 ga watan Mayu 2024.
Ga jihar Edo, “Za a wallafa jerin sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 23 ga watan Afrilu 2024 yayin da jam’iyyun siyasa za su fara yakin neman zabe a bainar jama’a a ranar 24 ga watan Afrilu 2024 kuma ya ƙare sa’o’i 24 kafin ranar zabe a ranar 19 ga watan Satumba 2024.”
A cewar sanarwar, kafin zaben Ondo, “Za a wallafa jerin sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 18 ga watan Yuni 2024 yayin da jam’iyyun siyasa za su fara yakin neman zabe a bainar jama’a a ranar 19 ga watan Yuni 2024 kuma zai kare sa’o’i 24 kafin ranar zabe a ranar 14 ga watan Nuwamba 2024.”
Hukumar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su lura da ayyukan a cikin Jadawalin don a bi su sosai.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Tantance Sabon Gwamnan CBN da Wasu Mutane Hudu
Yanzu haka dai majalisar dattawa ta fara tantance Dr Olayemi Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya CBN.
Haka kuma bayan tantance Cardoso akwai wasu mutane hudu da aka nada a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin CBN.