Muna da ƙararraki 39,526 da ke jiran mu yanzu haka – Shugabar Kotun ɗaukaka ƙara
Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya Justice Monica Dongban Mensem ta koka akan ƙararraki kimanin 39,526 da ke jiran hukunci a gaban kotun.
Mai shari’a Dongban Mensem ta lura cewa yawancin shari’o’in da aka shigar a kotun suna da alaka da rikicin zaɓe.
Ta ce danbarwar shari’ar zaɓe a kotunan ƙasar nan na zama abin damuwa, Yana kuma haifar da naƙasu a fannin tattalin arziƙi, tana mai cewa ɗaukacin tsarin shari’ar Najeriya na cike da ƙararrakin zaɓe wanda ke jiran hukunci da yanke hukunci kusan duk shekara.
Ta yi magana ne a wani zama na musamman na kotu da kotun ta ɗaukaka ƙara ta gudanar don bikin fara shekarar shari’a ta 2023/2024.
A cewar ta “Yana da matukar damuwa cewa Alƙalan kotunan da ke shari’a sun shafe watanni shida suna gudanar da shari’o’in zaɓe na musamman.
KARANTA NAN:INEC ta Sanya Ranakun Gudanar da Zabukan Gwamnoni a Wasu Jihohi 2
Ta kuma ce, kamata ya yi ƴan Siyasa su mai da hankali kan tsarin dimokuradiyya na cikin gida da kuma yin aiki da ruhin aminci ga juna, wanda hakan zai samar da maslahar da jituwa.
Sannan ta ce, Dukkanin zaɓuka basu bukatar a karƙare su a Kotu.
Dole ne mu tuna cewa ɓangaren Shari’a na saka ido ke akan abinda yake dai-dai da kuma akasin haka.
Don haka dole ne mu ci gaba da yin haɗin gwiwa don samar da ingantaccen tushe na dimokiradiyya ga al’ummarmu wajen ba da gudummawar da kundin tsarin mulki ya ba mu don samun cikakken yanayin zamantakewa mai kyau.
Mai shari’a Dongban Mensem ta bayyana cewa bayan zaɓen 2023 an kafa kwamitoci 98 a gaban kotuna daban-daban da ke da alhakin gudanar da kararraki 1,209 da aka shigar.
Daga cikin waɗannan korafe-korafen ta ce biyar an mika wa sashen PEPC, inda ƙararraki 147 akan zaɓen Sanatoci, 417 na ‘yan Majalisar wakilai, 557 da ke da alaka da ‘yan Majalisar Jiha, yayin da 83 ke kan zaɓen Gwamna.
Jihohi 28 ne suka halarci zaben Gwamna kuma an shigar da kara a Jihohi 24 daga cikin su.
Mun riga mun karbi kararraki da dama kafin zaɓen wanda suka shafi yadda ake gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun Siyasa a waɗannan Jihohin, kuma muna aiki tukuru don ganin an kammala su cikin gaggawa,” in ji ta.
Ta kuma bayyana cewa an ɗaukaka ƙara a gaban kotun kimanin 7,295, da kuma wasu 3,765 a shekarar 2022/2023, yayin da 5,617 daga cikinsu aka yi watsi da su.
Yayin da aka yi watsi da 1,030 na waɗannan kararraki kuma an ba 10,381 damar Kotun har yanzu tana da jimillar ƙararraki 39,526 da ke jiran ta tun daga ranar 31 ga Agustan 2023.