- Gwamnatin tarayya ta ce babu wani shiri na kara haraji a harkar sufurin jiragen sama a Najeriya
- Gwamnati za ta yi kokarin dakile duk wata barakar kudaden shiga a bangaren sufurin jiragen sama
- Gwamnati ta himmatu wajen samar da tsare-tsare da manufofin da za su zaburar da hannun jari a cikin harkar jiragen sama
Gwamnatin tarayya ta ce babu wani shiri na kara haraji a harkar sufurin jiragen sama a Najeriya, Daily Post ta rawaito.
Sai dai ministan ya ba da tabbacin cewa gwamnati ta himmatu wajen sake fasalin harkokin sufurin jiragen sama na kasar da ajandodin sa guda biyar.
KARANTA WANNAN: IGP Ya Baiwa Iyalan Jami’ai 420 da Suka Mutu Tsabar Kudi Naira Biliyan 1.3
Ya kuma yi nuni da cewa gwamnati za ta yi kokarin dakile duk wata barakar kudaden shiga a bangaren sufurin jiragen sama.
“Na yi nazarin ci gaban da aka samu zuwa yanzu dangane da gibin da ake da shi. Don haka, mun riga mun duba wuraren da aka fi mayar da hankali a kan batutuwa biyar, wato tsananin bin dokoki da ka’idoji na kasa; wajibcin kasa da kasa, haɓaka abubuwan more rayuwa don dacewa da fasinja, tallafawa haɓakawa da wadatar kasuwancin jiragen sama na cikin gida, da haɓaka ƙarfin ɗan adam, da haɓaka samar da kudaden shiga.
“A matsayina na ministan sufurin jiragen sama da sararin samaniya, na jajirce sosai kan wannan ajanda. A cikin waɗannan lokuttan ƙalubale, waɗanda ke tattare da haɓakar kasuwanni da rashin tabbas na duniya, buƙatar sake fasalin sashin zirga-zirgar jiragen sama don ci gaba mai ɗorewa bai taɓa kasancewa mai matsi ba. Yana buƙatar hangen nesa, juriya, kuɗi, da haɗin gwiwa.
“Ina da kwarin gwiwa cewa masu ruwa da tsaki da ke halartar zaman gidan yanar gizo na yau za su gina kan tarihinsu masu kishi don samar da dabarun da suka dace don sake fasalin fannin jiragen sama don samar da kudaden shiga da kuma ci gaba ta hanyar amfani da doka.
“A matsayinmu na gwamnati, mun himmatu wajen samar da tsare-tsare da manufofin da za su zaburar da hannun jari a cikin sarkar darajar jiragen sama,” inji shi.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Najeriya da Benin Sun Rasa Damar Karbar Bakuncin Gasar AFCON 2027
Yunkurin Najeriya na karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2027 da Jamhuriyar Benin ya ci tura
Hakan ya biyo bayan matakin da hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta dauka na bai wasu kasashen
CAF ta kuma tabbatar da cewa wata kasar afirka za ta karbi bakuncin gasar ta 2025
Yunkurin Najeriya na karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2027 da Jamhuriyar Benin ya ci tura.
Hakan ya biyo bayan matakin da hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta dauka na bai wa kasashen Kenya da Uganda da Tanzania dama.