- Hukumar NiMet ta yi hasashen yanayin samun rana da tsawa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a fadin kasar nan
- Yana da matukar muhimmanci jama’a su yi taka tsantsan don gujewa lafkuwar ambaliya
- Jama’a su kwashe duk wasu magudanan ruwa don kaucewa duk afkuwar wata matsala
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayin samun rana da tsawa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a fadin kasar nan.
Hasashen yanayi na NiMet da aka fitar a ranar Juma’a a Abuja ya yi hasashen sararin samaniya zai kasance cikin karancin gajimare a yankin arewa.
KARANTA WANNAN: Zaben Gwamna: Dubban Magoya Bayan PDP da LP sun Koma APC don Neman Mafita
Kamar yadda NiMet ta rawaito, ana iya samun tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Kaduna, Bauchi, Gombe, Sokoto da kuma Kebbi da safe.
“Washegari kuma ana sa ran samun tsawa a sassan jihohin Jigawa, Bauchi, Adamawa, Yobe, Taraba, Gombe, Sokoto, Zamfara, Kano da Katsina idan Allah ya amince.
“An yi hasashen sararin samaniya zai kasance da hasken rana da gajimare a yankin Arewa ta Tsakiya inda za a yi tsawa a sassan babban birnin tarayya, jihohin Nasarawa, Neja da Filato da safe.
“A washegari, ana hasashen samun tsawa da bugawar hadiri a sassan Plateau, Kogi, Benue, Kwara da kuma babban birnin tarayya,” in ji NiMet.
NiMet ta yi hasashen yanayi mai cike da gajimare a kan jihohin Kudu da na bakin teku da ake hasashen za a yi tsawa da ruwan sama a wasu sassan Oyo, Osun, Edo, Ondo, Cross River, Akwa Ibom, Legas da kuma Ribas da safiya.
An yi Hasashen samun tsawa da ruwan sama a wasu sassan jihohin Oyo, Ondo, Ekiti, Osun, Ogun, Edo, Ebonyi, Enugu, Abia, Anambra, Imo, Lagos, Bayelsa, Ribas, Delta, Cross River da kuma Akwa Ibom idan Allah ya yarda.
“A ranar Asabar, ana sa ran sararin samaniya zai kasance cikin hasken rana tare da gajimare jefi-jefi a kan yankin Arewa tare da yiwuwar yin tsawa a sassan jihohin Adamawa, Bauchi, Gombe, Kaduna, Zamfara, Taraba da Kebbi da safe.
“Ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Kaduna, Kano, Katsina, Gombe, Yobe, Borno, Zamfara, Sokoto da Bauchi da rana da kuma yamma idan Allah ya amince.
“Ana sa ran sararin samaniyar zai kasance cikin yanayin hasken rana tare da gizagizai a yankin Arewa ta Tsakiya da yiwuwar yin tsawa a safiya a sassan Babban Birnin Tarayya, Neja, Nasarawa da Jihohin Benue,” in ji ta.
A cewarta, ana hasashen za a yi tsawa a sassan babban birnin tarayya, Nasarawa, Filato, Kogi, Kwara da kuma Binuwai.
NiMet ya yi hasashen cewa za a yi hadari a kan garuruwan da ke cikin kudancin kasar nan da kuma jihohin da ke gabar teku tare da yiwuwar samun tsawa da ruwan sama a sassan jihohin Legas da Bayelsa da Akwa Ibom da Cross River da kuma jihar Rivers da safe.
Idan Allah ya amince an yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a sassan Ebonyi, Imo, Oyo, Osun, Edo, Ondo, Enugu, Anambra, Ogun, Lagos, Rivers, Bayelsa, Delta, Cross River da Akwa Ibom.
Hukumar ta yi hasashen sararin samaniya a ranar Lahadi zai kasance mai karancin gajimare a yankin Arewa da ake hasashen za a yi tsawa a sassan jihohin Adamawa, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Taraba.
“Bayan nan da rana, ana sa ran sararin samaniya zai kasance cikin yanayin rana tare da gajimare za su mamaye yankin Arewa ta tsakiya inda za a yi tsawa da bugawar hadari a sassan jihohin Neja, Filato da Kwara da safe.
“Daga baya da rana, ana sa ran sararin samaniya zai kasance cikin yanayin rana tare da gajimare jefi jefi.
“Ana sa ran samun iska a cikin biranen Kudu da bakin teku tare da yiwuwar samun tsawa a kan jihohin Oyo, Ondo, Ogun, Osun, Ado Ekiti, Lagos, Bayelsa da Rivers da safe,” in ji shi.
NiMet ta yi hasashen yanayin da ake ciki a yankin tare da yiwuwar yin tsawa a jihohin Imo, Enugu, Ebonyi, Anambra da Abia.
A cewar NiMet, matsakaicin ruwan sama na iya haifar da ambaliyar ruwa. An shawarci jama’a da su yi taka tsantsan don gujewa tuki da tafiya cikin ruwan ambaliya.
“Ta yiwu a samu iska mai karfi tare da haifar da tsawa musamman yankin Arewa. An shawarci ‘yan ƙasa da su ɗauki matakan tsaro da suka dace.
“Masu kula da Hatsarin Bala’i, Hukumomi da daidaikun jama’a su tashi tsaye wajen dakile asarar rayuka da dukiyoyi a lokacin damina.
“An shawarci duk ma’aikatan jirgin da su amfana da rahoton yanayi / faɗakarwar yanayi lokaci-lokaci daga NiMet don ingantaccen shirin su don ayyukansu,” in ji ta.
A wani labarin kuma,‘Yan Sanda Sun Kame Wani da Ake Zargin Ya Kware Wajen Damfara da ATM
Rundunar ‘yan sandan Yobe ta kama wani da ake zargin dan damfara ne da ke zagayawa wuraren cirar kudi na ATM domin damfarar mutane
Matashin da ake zargi ya kware wajen amfani da wannan dama wajen yashe kudaden dake cikin asusunsun wadanda abun ya shafa
Tuni dai sa’a ta kwace wa mai laifin a lokacin da aka kama shi ya yin da yake kokarin sauya katin ATM na wani
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama wani da ake zargin dan damfara ne da ke zagayawa wuraren cirar kudi na ATM a fadin jihar domin damfarar mutanen da ba su ji ba basu gani ba.
Matashin wanda ake zargi yana amfani da wannan dama wajen yashe kudaden dake cikin asusunsun wadanda abun ya shafa.