- Rundunar ‘yan sandan Yobe ta kama wani da ake zargin dan damfara ne da ke zagayawa wuraren cirar kudi na ATM domin damfarar mutane
- Matashin da ake zargi ya kware wajen amfani da wannan dama wajen yashe kudaden dake cikin asusunsun wadanda abun ya shafa
- Tuni dai sa’a ta kwace wa mai laifin a lokacin da aka kama shi ya yin da yake kokarin sauya katin ATM na wani
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama wani da ake zargin dan damfara ne da ke zagayawa wuraren cirar kudi na ATM a fadin jihar domin damfarar mutanen da ba su ji ba basu gani ba.
Matashin wanda ake zargi yana amfani da wannan dama wajen yashe kudaden dake cikin asusunsun wadanda abun ya shafa.
KARANTA WANNAN: Najeriya Na Bukatar Likitoci 250k Don Cika Ma’aunin WHO – WMA
Kakakin ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim a cikin wata sanarwa da ya fitar, ta bayyana cewa, “A ranar 27 ga watan Satumba, 2023 da misalin karfe 13:00 na rana, hukumar leken asiri ta jihar (SIB) ta kama wani mai suna Justice Gibson mai shekaru 28, dan Karim Lamido, jihar Taraba a ATM din First Bank dake kusa da titin Gashua a Damaturu.
“An ce ya mallaki katinan ATM daban-daban daga bankuna daban-daban da ake amfani da su wajen yin musaya da su bayan damfarar wadanda ba a san ko su wanene ba a wuraren ATM.
Sai dai kuma sa’a ta kwace wa mai laifin a lokacin da aka kama shi ya yin da yake kokarin sauya katin ATM na wani Musti Kafa.
“Mai laifin ya amsa laifin damfarar mutane da katinan ATM dinsu a wuraren ajiyar kudi na ATM ta hanyar zagayawa don duba duk wani mutum da ya kasa amfani da na’urar ta ATM inda kuma mai laifin yake taimakawa masu irin wannan matsala.
“A cikin haka sai ya samu lambobin sirri na PIN dinsu sannan daga karshe ya canza katin sannan ya ba da dalilan barin wani ATM na daban ya bar wanda abin ya shafa da shi da katin ATM na bogi ya cire duk kudin da ke cikin asusun.
“A kan haka ne Kwamishinan ‘yan sanda, CP Garba Ahmad, ya ba da shawarar cewa mutane su yi taka-tsan-tsan a lokacin da suke a ATMs kan irin wadannan nau’ukan masu laifi.”
Kakakin ‘yan sandan ya tabbatar da cewa rundunar ta himmatu wajen yaki da irin wadannan laifuka a rumfunan ATM dake fadin jihar.
A wani labarin kuma, WHO ta saki dala miliyan 16 don magance cutar kwalara
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da dala miliyan 16 daga asusun ba da agajin gaggawa na WHO don magance cutar kwalara.
Darakta-Janar na WHO, Dr Tedros Ghebreyesus ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ta yanar gizo.