- Manyan jiga-jigan jam’iyyar LP, a jihar Imo, a ranar Juma’a, sun mamaye ofishin INEC domin nuna rashin amincewarsu da kwamishinan zabe, REC
- Hanya daya tilo da za a tabbatar da sahihin zabe a jihar ita ce a tsige kwamishinan zaben REC na jihar
- Tuni dai INE ta sha alwashin gudanar da ingantaccen zabe a jihar
Manyan jiga-jigan jam’iyyar Labour Party, LP, a jihar Imo, a ranar Juma’a, sun mamaye ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, tare da nuna rashin amincewarsu da kwamishinan zabe, REC, Sylvia Agu, inda suka bukaci a tsige shi gabanin zaben ranar 11 ga watan Nuwambar 2023, Vanguard ta rawaito.
Shugaban LP na jihar, Callistus Ihejiagwa ne ya jagoranci zanga-zangar a ofishin INEC dake kan titin Owerri-Port Harcourt a Owerri.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Kotun Zabe Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Delta
Dalilinsu ya ta’allaka ne kan zargin rashin amincewa da yadda kwamishinan zabe na INEC a zaben Majalisar Dokoki ta Jiha da ya gabata inda ba a bi hanyoyin gudanar da zaben yadda ya kamata ba. Ya dage cewa hanya daya tilo da za a tabbatar da sahihin zabe a Imo ita ce a tsige REC.
Ya ce: “Hanya daya tilo da za a iya tabbatar da sahihin zaben gwamna a jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba ita ce hukumar ta gaggauta sake tura sabon REC a jihar.
“Jam’iyyar ta daina jin dadin REC a halin yanzu a Jihar biyo bayan abin da muka lura a lokacin zabukan ‘yan majalisar dokoki, da kuma zabukan ‘yan majalisun kasa inda ba a bi ka’idojin INEC ba.
“Abin da muke nema abu ne mai sauki, a cire REC kuma ku bi ka’idojin zabe da kuka gindaya. Mun gaji da ‘yan siyasa da ke rike da mukaman shugabanci ta bayan gida, Ya isa ya isa haka.
“Jam’iyyarmu za ta ci gaba da zaman lafiya kuma za ta ci gaba da neman a yi abubuwan da suka dace domin ci gaban Jihar.”
Da yake mayar da martani a madadin hukumar, shugaban sashen wayar da kan masu kada kuri’a a ofishin INEC na jihar, Emmanuella Opara, ya ce sun godewa shugabannin jam’iyyar LP da yadda suka gudanar da kansu tare da tabbatar wa jam’iyyar a shirye ta ke na gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana a jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Sannan ya kara da cewa hukumar ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen gudanar da sahihin zabe a jihar.
A wani labarin kuma, NiMet Tayi Hasashen Samun Hasken Rana da Tsawa Na Kwanaki 3
Hukumar NiMet ta yi hasashen yanayin samun rana da tsawa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a fadin kasar nan
Yana da matukar muhimmanci jama’a su yi taka tsantsan don gujewa lafkuwar ambaliya
Jama’a su kwashe duk wasu magudanan ruwa don kaucewa duk afkuwar wata matsala
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayin samun rana da tsawa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a fadin kasar nan.
Hasashen yanayi na NiMet da aka fitar a ranar Juma’a a Abuja ya yi hasashen sararin samaniya zai kasance cikin karancin gajimare a yankin arewa.