- Gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin kayan abinci da wanda bana abinci ba na miliyoyin naira ga ‘yan gudun hijira
- Yin watsi da waɗanda ke gudun hijira na iya haifar da babban sakamako
- An bayar da tallafin ne domin tunawa da ranar samun ‘yancin kai na shekarar 2023
Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta bayar da tallafin kayan abinci da wanda bana abinci ba na miliyoyin naira ga ‘yan gudun hijira a babban birnin tarayya Abuja.
Da yake gabatar da kayayyakin ga ‘yan gudun hijira a Abuja, Kwamishinan Tarayya, Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira NCFRMI Alhaji Tijani Ahmed, ya ce sun bayar da tallafin ne domin tunawa da ranar samun ‘yancin kai na shekarar 2023.
KARANTA WANNAN: An Gano Jabun Wasiƙun Ɗaukar Aiki A Gwamnatin Filato
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin sun kasance ‘yan gudun hijira a sansanin Durumi, New Karshi da Wassa a babban birnin tarayya Abuja.
‘Yan gudun hijirar dai sun fito ne daga Gwoza da ke Borno da Adamawa da wasu da suka koma Abuja, sakamakon rikicin Boko Haram da ya addabi yankin Arewa maso Gabas.
Da yake jawabi ga ‘yan gudun hijirar, Ahmed ya nanata kudurin shugaban kasa Bola Tinubu na tabbatar da hadin kai tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da samar da kirkire-kirkire da kuma neman mafita mai dorewa ga duk wanda abin ya shafa.
“A yau, mun hallara a Durumi, Abuja, a kan aikin mika hannu ga wadanda ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira na Durumi. Manufarmu ita ce mu ba da tallafi mai mahimmanci ta hanyar kayan aikin gona, kayan ilimi da buhunan abinci.
“Yayin da al’ummarmu ke bikin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai, mun sabunta alkawarinmu na magance matsalolin da ‘yan gudun hijirar ke ciki.
Ƙudurinmu a bayyane yake: babu wanda, ko da kuwa jinsinsa, shekaru, ko rauninsa, da ya kamata a bar shi ba tare da tallafi mai mahimmanci ba, yana mai bayyana ajandar ‘Sabuwar bege’ na Shugaban ƙasa.
“Muhimmancin bayar da tallafi ga ‘yan gudun hijira ba za a iya wuce gona da iri ba. Yin watsi da waɗanda ke gudun hijira na iya haifar da babban sakamako na zamantakewa da tattalin arziƙin ga waɗanda suka rasa matsugunansu da kuma al’ummominsu da ke masaukinsu,” in ji shi.
A cewarsa, a yayin da ake fama da rikice-rikicen ƙaura da suka daɗe suna shafar ‘yan gudun hijirar, tabbatar da samun taimako a irin wannan lokacin yana da matuƙar mahimmanci.
“Bisa da dabarun magance dorewar hukumar da kuma sadaukar da kai ga jin dadin al’ummomin da suka karbi bakuncinsu, muna alfaharin sanar da samar da muhimman kayan aikin noma.
“Wadannan tsare-tsare na nufin karfafawa al’ummar mu da suka yi gudun hijira, wadanda yawancinsu kwararrun manoma ne, don sake gina rayuwarsu.
“Bugu da ƙari, mun himmatu daidai da samar da Kayayyakin Ilimi don tabbatar da cewa yara da matasa na IDP sun sami damar samun kayan koyo, don sauƙaƙe ci gaban ilimi da haɓaka su.
“Bugu da ƙari, muna rarraba fakitin kula da abinci don rage yunwa cikin gaggawa da kuma samar da abubuwan da ake bukata ga mabukata,” in ji shi.
Kayayyakin ilimi da aka bayar sun hada da dozin 400 na littattafan rubutu, takalman makaranta 180, fararen allunan rubutu guda 10 da kuma abun goge allo guda 10.
Sauran sun hada da jakunkuna na makaranta guda 180 na musamman, tebura da kujeru 180 na roba na musamman, biro da kuma fensir.
An kuma baiwa ‘yan gudun hijirar kayayyakin amfanin gona irinsu maganin kashe kwari guda 26, maganin ciyawa guda 26, maganin kwari guda 26, injin feshin magani guda 86 da famfunan ban ruwa guda 25.
A yayin da kayayyakin abincin sun hada da buhu 97 na shinkafa mai nauyin kilogiram 25kg, katon din spaghetti 97, buhu 97 na Semovita mai nauyin 1kg katan 20 na man abinci, katan 26 na maggin dunkule da kuma katon 22 na gishiri.
A madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Shugaban sansanin Durumi Ibrahim Ahmad ya yabawa Gwamnatin Tarayya bisa wannan tallafin. NAN
A wani labarin kuma, Ministan Gidaje Ya Yabawa Kamfanin BUA
Ministan gidaje da raya birane Ahmed Musa Dangiwa ya yabawa kamfanin siminti na BUA a kan matakin rage farashin siminti
Tashin gwauron zabbi na farashin kayayyakin gine-gine, musamman siminti, ya kawo cikas wajen mallakar gidaje
Wannan ya yi dai dai da samar da gidaje masu rahusa a matsayin babban fifiko bisa tsarin sabunta bege na shugaban kasa
Ministan gidaje da raya birane Arc Ahmed Musa Dangiwa ya yabawa kamfanin siminti na BUA a kan matakin rage farashin siminti daga kusan N5,500 zuwa Naira N3,500.
Ya ce, matakin da kamfanin ya dauka a matsayin wani shiri ne da zai taimaka matuka wajen rage farashin siminti, wanda ke da tsada wajen gina gidaje.