- Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN reshen jihar Ondo ta yi kira da a dauki matakin gaggawa daga gwamnatin jihar da jami’an tsaro don ganin an sako mawakin Cocin CAC Oke-Igan
- CAN tace wadanda suka aikata wannan danyen aiki za su fuskanci fushin Allah
- CAN ta jaddada bukatar gaggauta shiga tsakani domin kawo karshen wannan aika-aika
Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN reshen jihar Ondo, a ranar Talata, ta yi kira da a dauki matakin gaggawa daga gwamnatin jihar da jami’an tsaro don ganin an sako mawakan Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Oke-Igan dake Akure babban birnin jihar.
Shugaban CAN na jihar Ondo, Revd. Uba Anselm Ologunwa, shi ne wanda ya bayyana damuwar kan yadda ake samun yawaitar sace-sacen mutane a yankin Ifon a karamar hukumar Ose ta jihar, ya jaddada bukatar gaggauta shiga tsakani domin kawo karshen wannan aika-aika.
KARANTA WANNAN: FG ta Bada Gudummawar Abinci, Kayan Aikin Noma Ga ‘Yan Gudun Hijira
Ologunwa ya bayyana sace mawakan 25 a matsayin wani abu da ya saba wa ka’idar dan Adam.
A wata ziyarar jaje ga babban Sufuritandan yankin na CAC, Fasto Benjamin Akanmu, Uban Rabaran ya bada tabbacin cewa daukacin kiristoci a jihar sun tashi tsaye wajen addu’a da kokarin ganin an sako ‘yan kungiyar mawakan da aka sace.
Shugaban CAN ya ci gaba da cewa wadanda suka aikata wannan danyen aiki za su fuskanci fushin Allah.
Ologunwa ya kuma yabawa cocin, jami’an tsaro, da kuma iyalan wadanda abin ya shafa saboda jajircewa da kokarin da suka yi na shawo kan lamarin.
Ya amince da kokarin hadin gwiwa da ake yi don ganin an dawo da mawakan da aka sace cikin koshin lafiya.
A nasa jawabin, Sufuritandan yankin na CAC, Fasto Akanmu, ya bayyana cewa kungiyar mawakan na kan hanyar zuwa Ifon ne domin halartar jana’izar mahaifin malamin cocin, wanda ya gudana a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya bayyana cewa wasu gungun masu garkuwa da mutane biyar ne suka tare su a wani sashe na hanyar da ba ta da kyau.
Faston na CAC ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun yi harbin kan motar da mawakan ke tafiya a ciki sannan suka tilasta su kutsawa da su cikin daji.
Ya kara da cewa cikin ikon Allah takwas daga cikin mawakan sun samu kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Sai dai sauran wadanda aka abin ya shafa suna hannun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Fasto Akanmu ya ci gaba da bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci cocin da iyalan mawakan da aka sace su biya kudin fansa naira miliyan 50.
A wani labarin kuma, An Gano Jabun Wasiƙun Ɗaukar Aiki A Gwamnatin Filato
Kwamiti da gwamnan Filato Caleb Mutfwang ya kafa ya bayyana cewa an fitar da wasikun daukar ma’aikata na bogi a ma’aikatun jihar
Duk da barazanar da mutane da kungiyoyin masu ruwa da tsaki ke yi a kan lamarin bai hana kwamitin gudanar da aikin sa ba
An kafa kwamitin domin duba aikin daukar ma’aikata na karshe da gwamnatin da ta shude ta gudanar
Wani kwamiti da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya kafa ya bayyana a Jos a ranar Talata cewa an fitar da wasikun daukar ma’aikata na bogi a ma’aikatun jihar, kafin hawan gwamnatinsa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an kafa kwamitin mai mutane 15 a ranar 26 ga watan Yuli domin duba aikin daukar ma’aikata na karshe da gwamnatin da ta shude ta gudanar.