- Jami’an rundunar shiyyar Enugu na Hukumar EFCC, sun kama wasu mutane 32 da ake zargi da damfarar ta internet
- An kama su ne bisa wasu sahihan bayanan sirri kan ayyukan da suke aikatawa
- Za a gurfanar dasu gaban kuliya domin su girbe abinda suka shuka
Jami’an rundunar shiyyar Enugu na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, sun kama wasu mutane 32 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wani samame da suka yi a lokaci guda a Awka, jihar Anambra da kuma garin Enugu na jihar Enugu.
Wadanda ake zargin sun hada da Stanley Okechukwu, Chukwudi Michael, Nnaife Onyedika, Nnamdi Christian, Pascal Akachukwu, Ekeme Christian Luke, Denis Chidozie da kuma Ebuka Mmaduka.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: PDP Ta Sha Kaye Yayin Da Kotu Ta Tabbatar Da Wanda Ya Lashe Zaben Abia
Sannan akwai: Ekene Excellent, Emmanuel Okochi Osita, Akunne Prince Ikenna, Igwe Nnaemeka Shedrack, Nonso Henry Ozo Ekwe, Ebuka Obike Boniface, Goodluck Ameachi Ifeanyi, Hillary Chiemele Chukwudizie, Chinedu Onwuegbusi Ignitus, Onuoha Ifeanyi Anthony.
Sauran sun hada da: Bassey Nnolue Jason, Chinedu Nnolue Kingsley, Okpe Matthew, Emmanuel Abonyi, Igwenagu Kenechukwu Collins, Joachim Okpe, Kelechi Ibenyenwa, David Chiemerie, Kingsley Ngwu, Ndubuisi Anthony, Collins Chidubem, Innocent Chisom, Kalu Nnachi da Chukwuemeka Henry.
An kama su ne bisa wasu sahihan bayanan sirri kan ayyukan da ake zarginsu da aikata laifukan da suka shafi damfarar intanet.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sune wayoyin hannu, kwamfutocin tafi da gidanka da motoci guda biyu: Lexus ES 350 da Lexus RX 330.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala cikakken bincike.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Wasu Mutane 6 a Gaban Kotu Bisa Zargin Sata
Rundunar ‘yan sandan a ranar Juma’a, ta gurfanar da wasu mutane shida a gaban wata kotun Majistare ta Ojo da ke jihar Legas
Ana zargin masu laifin sun aikata mummunar barna kan kayan da suka sace
Tuni suke fuskantar tuhuma kan wannan aika-aika
Rundunar ‘yan sandan a ranar Juma’a, ta gurfanar da wasu mutane shida a gaban wata kotun Majistare ta Ojo da ke jihar Legas bisa zargin su da kutsawa cikin wani gida da nufin yin sata.
Wadanda ake tuhumar su ne Salisu Musa mai shekaru 36; Awolu Isa mai shekaru 48; Sani Ibrahim dan shekara 28; Suraju Yunusa, 36; Habibu Yunus 28 da Usman Musa mai shekaru 28.