- Gwamnatin Kano ta baiwa Malam Dayyabu Bala Gezawa aiki na dindindin, da kujerar Hajji gami da kudade
- Kuɗaɗen da aka mayar dai sun kasance wani ɓangare ne na tallafin tafiye tafiye na alhazai na wata ƙaramar hukuma ta jihar
- Duk da matsalolin tattalin arziki da mutumin yake ciki bai hana shi mayar da makudan kudaden ba
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana a ranar Talata cewa ta baiwa Malam Dayyabu Bala Gezawa aiki na dindindin, da kujerar Hajji, da kuma kudi naira miliyan daya.
Gezawa, ma’aikaci ne mai zaman kansa a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ya samu tukwuicin gaskiya ne bayan ya dawo da dala miliyan 16.
KARANTA WANNAN: Majalisa Ta Yi Allah-Wadai da Haramtattun Shingayen Bincike,Karbar Kudin Ababen Hawa
Rahotanni sun bayyana cewa Gezawa ya samu kudaden ne a lokacin da yake bakin aiki, inda ya mayar wa babban daraktan hukumar.
Kuɗaɗen wani ɓangare ne na tallafin tafiye tafiye na alhazai na wata ƙaramar hukuma ta jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, a yayin gabatar da rahoton aikin hajjin 2023 da hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta yi, ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar ba shi ladan ne domin nuna godiya ga gaskiyarsa.
“Wannan ma’aikacin da ba ya aiki ya tabbatar da amincinsa ta hanyar mayar da kudaden da suka bace, duk da matsayinsa da matsalolin tattalin arziki a kasar,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Gwamna Zulum Ya Mayar da Makarantar Larabci Zuwa Cibiya Ta Musamman
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da mayar da kwalejin koyan larabci ta zuwa wata cibiya ta musamman ta koyar da ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci
Sabuwar cibiyar za a gudanar da ita ne tare da hadin gwiwar jami’ar Al-Azhar kuma za ta samar da daliban da za su dinga wa’azi da zai dakile akidar Boko Haram
Gwamnan ya umurci sabuwar hukumar ilimin Larabci da Tsangaya da ta karbi ragamar tafiyar da dukkanin makarantun Tsangaya da na islamiyya a jihar
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da mayar da kwalejin koyan larabci ta Mustapha Umar Elkanemi da ke Maiduguri zuwa wata cibiya ta musamman ta koyar da ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci da nufin dakile akidar Boko Haram.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafofin yada labarai, Isa Gusau ya fitar, ya bayyana hakan a ranar Talata a lokacin da ya kai ziyarar duba kwalejin, domin shirye-shiryen sauya sheka.