- Matukar tana son saki, sai ta auro min wata matar
- Ba ni da Naira dubu 160,000 da zan ba shi, sai dai idan shi ma zai iya biya na kudin gamsar da shi da na yi a lokacin aure
- Matar ta garzaya kotu tana neman a raba aurenta da mijinta saboda rashin kulawa da mutuntawa
Wani dan kasuwa mai suna Yahaya Mohammed, ya shaida wa wata kotun Upper Area dake Kubwa, babban birnin tarayya Abuja cewa zai saki matarsa, Hauwau Hamza idan ta biya shi Naira N160,000.
Mohammed da Hamza sun yi aure ne bisa tsarin shari’ar Musulunci a shekarar 2020 kuma ba su da ‘ya’ya tare.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Benue Za ta Dauki Masu Dafa Abinci Sama da 6k Aiki
Tun da farko Hamza ta garzaya kotu tana neman a raba aurenta da Mohammed saboda rashin kulawa da mutuntawa.
“Idan tana son saki, sai ta auro min wata mata. Ina son matata ta biya ni duk abin da na kashe mata a bikin aurenmu.
“Na biya N60,000 a matsayin sadaki don in auri matata kuma na kashe Naira 100,000 na tufafinta, nace ta biya ni jimillar kudaden,” in ji shi.
Sai dai a martanin mai shigar da karar ta ce idan har ya dace a Musulunci ta aurawa mijinta wata matar kafin ya sake ta, sai ta yi hakan.
Ta kara da cewa Mohammed bai kashe mata kudi har N160,000 ba, inda ta ce sadakinta N60,000 ne kawai.
“Ba ni da Naira 160,000 da zan ba shi, sai dai idan shi ma zai iya biya na kudin gamsar da shi da na yi a lokacin aure da kuma girkin da na yi tsawon shekaru,” in ji mai karar.
Mohammed, ya ce idan mai karar ta ce ta gamsar da shi, shi ma ya kula da ciyar da ita da jin dadin auren.
Alkalin kotun, Mohammed Wakili ya ce bai dace a addinin Musulunci ba wanda ta shigar da kara ta sake samarwa wanda ake kara wata matar kafin ya sake ta.
Wakili ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Oktoba domin yanke hukunci
A wani labarin kuma,‘Yan Sanda Sun Kame Wani Yaro Bisa Laifin Binne Kaninsa da Ransa
Jami’an ‘yan sandan Kogi, sun cafke wani yaro Goodness Oshodi, dan shekara 19 bisa zargin binne kanensa mai suna Friday Oshhodi
Mahaifiyar yaron ta umurci babban danta da ya hukunta wanda abin ya shafa saboda sace mata Naira dubu N10,000
Kafin aiwatar da umurnin mahaifiyarsa wanda ake zargin ya fara lakadawa mai laifin dukan tsiya kafin ya yanke shawarar binne shi da ransa
Jami’an ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kogi, sun cafke Goodness Oshodi, wani yaro dan shekara 19, wanda ake zargin ya binne kanensa mai suna Friday Oshhodi da ransa bisa umarnin mahaifiyarsa kan satar Naira 10,000.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a unguwar Apamisede, dake karamar hukumar Adavi ta jihar.