- Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabuwar tawagar gudanarwar hukumar ICPC
- Sabon shugaban ICPC kafin wannan ya taba rike mukamin Babban Lauyan gwamnatin Jihar Jigawa
- Shugaban ya roki sabbin jami’an ICPC da su kasance kan gaba a kodayaushe yayin da suke gudanar da ayyukansu ba tare da nuna tsoro ko shakka ba
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabuwar tawagar gudanarwa ta hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran laifuka ICPC.
Wannan ya yi daidai da ikon da aka bai wa shugaban kasa kamar yadda aka kafa a sashe na 3 (6) na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaka ta shekarar 2000, da kuma ci gaba da wa’adin sabunta fata na sake fasalin manyan cibiyoyi da karfafa yakin da Najeriya ke yi da cin hanci da rashawa.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya nada Shugaban Hukumar NAHCON
Sabbin wadanda ICPC ta nada sun hada da Dakta Musa Adamu Aliyu a matsayin shugaba da babban jami’in gudanarwa da Clifford Okwudiri Oparaodu a matsayin sakataren hukumar.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ta ce an gabatar da sabon shugaban ne domin amincewar majalisar dattawan Najeriya.
Hakan ya biyo bayan amincewar shugaban kasa ne na bukatar shugaban mai barin gado daya ci gaba da hutun kafin karshen wa’adinsa daga ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023, gabanin cikar wa’adinsa a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2024.
Matsayin sakataren hukumar, ba ya bukatar amincewar majalisar dattawa, saboda haka, bisa umarnin shugaban kasa, nada Oparaodu a matsayin sakataren hukumar ya fara aiki nan take.
Aliyu, Babban Lauyan Najeriya wanda ya samu digirin digirgir a fannin shari’a, ya aiwatar da gyare-gyare masu nisa a matsayin Babban Lauyan Jihar Jigawa.
Oparaodu, lauya ne wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki wanda ya samu gogewa, ya yi aikin kwarai a aikin gwamnati a matsayin mamba a hukumar shari’a ta jihar Ribas kuma shugaban kwamitin riko na karamar hukumar birnin Fatakwal.
Shugaban ya roki sabbin jami’an hukumar ta ICPC da su kasance kan gaba a kodayaushe yayin da suke gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko fifita su ba dangane da duk wani abu da ke gabansu.
A wani labarin kuma, Ban Koma Jamus Domin Yin Jinya Ba – Gwamna Akeredolu
Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya caccaki mutanen da ke yada jita-jitar komawar sa kasar Jamus domin jinya
Gwamnan ya bayyana cewa labarin ba gaskiya bane kuma ba shi da tushe balle makama
Wannan jita-jitar na daya daga cikin dabarun da wasu ‘yan siyasa ke amfani da ita wajen tunzura jama’a kan gwamnan
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a ranar Talata ya caccaki mutanen da ke yada jita-jitar komawar sa kasar Jamus domin jinya a matsayin mugaye, da rashin kunya, da mayaudara, inda ya bayyana cewa suna yunkurin haddasa fargaba a jihar.