- Rundunar ‘yan sandan Ondo tana bin wani mutum mai matsakaicin shekaru, Kehinde Olanipekun, wanda ake zargi da raunata matarsa da adda
- Matar tace mijina ya raunata ni sau da dama saboda tunkararsa da nayi bisa cin zarafi da yunkurin kwana da diyar cikin sa yayin da bana gida
- Bayan faruwar lamarin na tunkari mijina wanda bai musanta hakan ba inda ya ba ni hakuri, ya yarda cewa ya yi kuskure kuma tare da alkawarin ba zai sake ba
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo tana bin wani mutum mai matsakaicin shekaru, Kehinde Olanipekun, wanda ake zargi da raunata matarsa Damilola Olanipekun da adda,kan kalubalantarsa kan wasu abubuwa na batsa da diyarsa.
An ce wanda ake zargin ya raunata matarsa sau da dama saboda tunkararsa da cin zarafi da yunkurin kwana da diyar sa yayin da matar ke tafiya bayan gari.
KARANTA WANNAN: Muna Samun Nasara a Yaki da Miyagun Kwayoyi, In Ji Kwamandan NDLEA
Makwabtan wadanda lamarin ya rutsa da su a unguwar Idashen cikin garin Owo a karamar hukumar Owo ta jihar ne suka garzaya da matar zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owo, amma sai aka garzaya da ita wani asibiti saboda girman raunukan da suka samu, yayin da mijin nata ya gudu.
Da take magana kan lamarin, Damilola ta bayyana cewa mijin nata ya rika lalata da ‘yarta, yana yunkurin lalata da ita kuma yarinyar ‘yar shekara 14 sai da ta kai mata rahoto a lokacin da matsin takurar baban nata ke kara yawa.
Matar da ta samu rauni ta ce yarinyar ba ta kai rahoton tsangwamar da aka yi mata da wuri ba don ceto aurenta amma sai da ta yi karfin hali ta gaya wa mahaifiyarta domin ta tabbatar da abinda maihaifinta ya yi na ci zarafinta a gidan.
Ta ce, “Na yi mamakin wannan fallasa, na fuskanci mijina wanda bai musanta hakan ba amma ya ba ni hakuri, ya yarda cewa ya yi kuskure kuma ya yi alkawarin ba zai sake yin irin wannan aikin ba.
Amma na yi mamakin ganin ya dawo gida jim kadan bayan ya tafi aiki bayan kwanaki uku da zargin ya ce ruwan sama ya yi tasiri a kasuwancinsa. Ya aika da yaran biyu gida rufe da leda ya shige daki.
Ya dawo falo da adda, ya ce yana so ya share gonarsa amma cikin lumshe ido, sai ya ja ni cikin dakin, ya kulle kofa sai ya fara buga mini addar dake hannun sa da dama.
“Ya ci gaba da bugu na, yayin da na yi ihun neman taimako amma an kulle kofar kuma sai da makwabta suka dauki mintoci da dama kafin su bude kofar sai ya kulle, ya bar ni cikin jinina.
“Sun garzaya da ni asibiti, sai na suma kafin a isa asibitin, sun kusa ki amincewa da ni saboda likitoci sun dauka na mutu har sai da suka gane cewa ina raye.”
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta kaddamar da farautar mijin wanda aka ce ya gudu ne nan take makwabta suka shiga dakin.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami’an ‘yan sandan na ci gaba da neman mutumin.
“Har yanzu muna neman mutumin. Ya gudu daga wurin da lamarin ya faru nan take mutanen da ke wajen suka ceto matar. Ina mai tabbatar muku da cewa nan da wani lokaci mai nisa za a kama shi,” inji ta.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Jakadan Najeriya a Morocco Ya Rasu
Jakadan Najeriya a Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, ya rasu.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari shine wanda ya nada marigayi Bamalli a matsayin jakadan a shekarar da ta gabata
Jakadan na Najeriya a Morocco ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar
Jakadan Najeriya a Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, ya rasu.
Bamalli, wanda Muhammadu Buhari ya nada a shekarar da ta gabata, shi ne Magajin Garin Zazzau, kuma kanin Sarkin Zazzau, a Kaduna.