- Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa Lionel Messi ne zai lashe kyautar Ballon d’Or
- Guardiola yace Ballon d’Or ta zama sashi biyu
- Idan ya lashe kyaur zai kawar da abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe sau biyar
Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa Lionel Messi ne zai lashe kyautar Ballon d’Or ta bana.
Guardiola ya yarda cewa duk da Erling Haaland ya zira kwallaye da yawa yayin da City ta lashe kofin a bara, Messi ya jagoranci Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya ta 2022.
KARANTA WANNAN: Chelsea ta Tabbatar da Cewa ‘Yan Wasa 2 Ba Za Su Buga Karawar Arsenal Ba
Ya shaida wa taron manema labarai a ranar Juma’a: “A koyaushe ina cewa Ballon d’Or ta zama sashi biyu. Daya na Messi daya na sauran.
“Haaland yakamata yayi nasara ko . Mun ci kwallaye uku, ya zura kwallaye miliyan. Ina son Erling ya yi nasara. Amma Messi… Leo ya lashe gasar cin kofin duniya!”
Ana kyautata zaton Messi ne zai lashe kyautar a karo na takwas a ranar 30 ga watan Oktoba.
Zai kawar da dan wasan mai shekaru 36 a kan abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe sau biyar.
A wani labarin kuma, Wani Magidanci Ya Raunata Matarsa Kan Kebewa da Diyar Cikinsa
Rundunar ‘yan sandan Ondo tana bin wani mutum mai matsakaicin shekaru, Kehinde Olanipekun, wanda ake zargi da raunata matarsa da adda
Matar tace mijina ya raunata ni sau da dama saboda tunkararsa da nayi bisa cin zarafi da yunkurin kwana da diyar cikin sa yayin da bana gida
Bayan faruwar lamarin na tunkari mijina wanda bai musanta hakan ba inda ya ba ni hakuri, ya yarda cewa ya yi kuskure kuma tare da alkawarin ba zai sake ba
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo tana bin wani mutum mai matsakaicin shekaru, Kehinde Olanipekun, wanda ake zargi da raunata matarsa Damilola Olanipekun da adda,kan kalubalantarsa kan wasu abubuwa na batsa da diyarsa.
An ce wanda ake zargin ya raunata matarsa sau da dama saboda tunkararsa da cin zarafi da yunkurin kwana da diyar sa yayin da matar ke tafiya bayan gari.