- Shugaban sabbin jami’an tsaro al’umma na jihar Sokoto, Kanal Garba Moyi mai ritaya, ya yi murabus daga mukaminsa
- Tson kanal din yi aiki a matsayin kwamishinan tsaro na jihar sau 3 daban-daban
- Abin takaici ne yadda wasu suka iya yin faifan bidiyo wanda ya fara yawo a shafukan sada zumunta don bata min suna
Shugaban sabbin jami’an tsaro al’umma na jihar Sokoto, Kanal Garba Moyi (mai ritaya), ya yi murabus daga mukamin nasa.
Moyi, wanda shi ne kwamishinan tsaro na jihar na wa’adi uku ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar ‘yan jarida ta Najeriya da ke Sokoto.
KARANTA WANNAN: Bauchi: Dalibai 240 Ne Za su Fafata a Gasar Karatun Al-Qur’ani ta 2023
Da yake magana a lokacin da yake zantawa da manema labarai, Kanal mai ritaya ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne biyo bayan wani rubutu da aka wallafa a shafin sada zumunta wanda ya ce an yi masa don a taba kimarsa.
“Na yi wa kasa hidima har na yi ritaya a matsayin Kanal daga nan na shiga siyasa na zama shugaban karamar hukuma ta.
“Na kuma yi aiki a matsayin kwamishinan tsaro na jihar sau 3 daban-daban har na yi murabus a gwamnatin da ta shude ba tare da wani aibu ba”
“Abin takaici ne yadda wasu suka iya yin faifan bidiyo wanda ya fara yawo a shafukan sada zumunta don bata min suna, ina ganin abin da ya fi dacewa shi ne na yi murabus.”
Sai dai ya yabawa gwamnan jihar Ahmed Aliyu Sokoto bisa ganin ya cancanci wannan aiki a karon farko.
A wani labarin kuma, IGP Egbetokun Yayi Allah-Wadai da Fashin Bankin Otukpo
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, ya yi kakkausar suka ga wani mummunan fashin da aka yi a bankin dake garin Otukpo na jihar Binuwai
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi gargadi tare da kaddamar da wani gagarumin aikin hadin gwiwa domin gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kotu
Tuni dai jami’an tsaro suka bindige wasu mutane biyu da ake zargin a lokacin da suke kokarin tserewa bayan aikata ta’asar
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, ya yi kakkausar suka ga wani mummunan fashin da aka yi a banki a garin Otukpo na jihar Binuwai, wanda ya yi sanadin salwantar rayukan jami’an ‘yan sanda da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
Egbetokun, a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Asabar, ya ce ta’addancin cin zarafi ne a kan ka’idojin zaman lafiya, tsaro, da adalci wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro ke aiki tukuru domin tabbatar da kawo karshe sa.