Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata shugaban kasa ya nada shugabannin hukumar zabe ba.
Jega ya bayyana hakan ne dalilin da ya sa yake magana a wani taron kwana biyu da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokaradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya wa sanatoci a garin Ikot Ekpene na jihar Akwa Ibom ranar Asabar.
Tsohon shugaban na INEC ya kuma yi kira da a yi gyara ga dokar zabe ta 2022.
A cewarsa, duk da cewa dokokin zaben Najeriya na yanzu za a iya cewa su ne mafi kyau a tarihin kasar, amma ba cikakkuu ba ne kuma akwai bukatar a kara yin gyare-gyare don kawar da shubuha, da fayyace da kuma karfafa wasu sassansa.
Karanta nanDole Ne Mu Dauki Matakai Masu Tsauri Idan Munason Nijeriya Ta Cigaba-Tinubu
Gyare-gyaren, in ji shi, ya kamata su sanya dokar fitar da sakamakon zabe ta yanar gizo dole daga zabukan da ke tafe a shekarar 2027.
Akan shugabancin hukumar ta INEC, Jega ya jaddada cewa kamata ya yi a hana shugaban kasa ikon nada shugaban da kwamishinonin INEC na kasa domin kwato hukumar daga bangaranci.
Ya ce kamata ya yi a sake duba dokar domin tabbatar da an warware duk wasu al’amura da suka taso daga gudanar da zabe tare da yanke hukunci kafin ranar da za a rantsar da su.
Masu ruwa da tsaki da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda sashe na 64 na dokar zabe, wanda ya bayyana yadda ake yada sakamakon zaben, yana da saukin yin magudi ta wannan hanyar.
INEC za ta sami isasshen lokacin da za ta shirya wa wannan doka, idan an yi wa dokar kwaskwarima da wuri a zaɓen da ke tafe inji shi.
Jega ya kuma yi kira da a bullo da ko dai a fara kada kuri’a ga wadanda suka cancanci kada kuri’a a kan aikin zabe, kamar su ma’aikatan INEC, masu sa ido da direbobinsu, jami’an tsaro, da ‘yan jarida ko kuma wani tsari na musamman da zai ba su damar kada kuri’a a ranar zabe, musamman zaben shugaban kasa.
A wani labarin kumaGobara Ta Janyo Asarar Kadarorin Miliyan 4 A Ilori
Tsohon shugaban na INEC ya yi kira ga ‘yan kasashen waje su kada kuri’a, a kalla don zaben shugaban kasa, don baiwa ‘yan kasa damar kada kuri’a, musamman wadanda ke aiki a kasashen waje.
Akwai bukatar a inganta shigar mata, idan ya cancanta da kashi 35 cikin 100 na mukamai masu zabe a majalisar dokoki, da kuma cikin jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyun siyasa in ji shi.