- Tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya samu nasara a karar da Salisu Yushau Abdullahi na Jam’iyyar NNPP ya shigar a kansa
- Shaidun mai shigar da kara sun ba da shaidar cewa ba a samu wani tashin hankali ba a lokacin zaben
- Alkalin kotun ya yi mamakin yadda dukkanin shaidun mai shigar da kara suka isa rumfunan zabensu daban-daban a lokaci guda kuma suka shaida yadda aka kada kuri’a
Tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya samu nasara a karar da Salisu Yushau Abdullahi na Jam’iyyar NNPP ya shigar a kansa, wanda ke neman soke zabensa na sake zama wakilin mazabar Doguwa/Tudunwada dake Kano.
Da yake yanke hukunci a karar da Abdullahi ya shigar a kan dan takarar jam’iyyar APC, Justice L.B. Owolabi, ya ce wanda ya shigar da karar ya kasa tabbatar da kokensa cikin shakkun da doka ta tanada.
KARANTA WANNAN: Tsohon Shugaban Kasa Ya Bada Shawarin Yadda Za a Gyara Ilimi
Mai shari’a Owolabi ya ce duk wasu dalilai guda uku da mai shigar da kara ya dogara da su – wato, na zargin Doguwa da cin hanci da rashawa, rashin bin dokar zabe, da rashin samun kuri’un da ake bukata na halal, ba su da tushe balle makama kuma ba za a amince da su a matsayin dalilan soke zaben ba.
Dangane da zargin tashe-tashen hankula a lokacin zabe, shaidu 21 na mai shigar da kara sun ba da shaida akasin haka, inda suka bayyana cewa ba a samu wani tashin hankali ba lokacin zaben.
Kotun, a cikin hukuncin da aka yanke, ta amince da cewa dukkan shaidu 32 da mai shigar da kara ya kira, sun kasa bayar da kwakkwarar hujjar da za ta iya dakile zaben.
A lokacin da yake gabatar da hukuncin, alkalin kotun ya yi mamakin yadda dukkanin shaidun mai shigar da kara suka isa rumfunan zabensu daban-daban a lokaci guda kuma suka shaida yadda aka kada kuri’a a dukkan sassan amma sun kasa gane takardar sakamakon zaben. Don haka shaidun su, in ji shi, ba za su iya jurewa gwajin lokaci ba.
“Mai shigar da kara gaba daya ya kasa yin duk wata shari’a da za ta iya kawar da zaben Alhassan Ado Doguwa; don haka an dawo da shi bisa ga zaben da kuri’u mafi rinjaye,” inji alkalin.
A wani labarin kuma, Wike Ya Ba da Umarnin Rusa Wata Shahararriyar Kasuwa
Yanzu haka dai ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ba da umarnin ruguza shahararriyar kasuwar COVID-19
Ruguje shagunan da matsugunan da suke ba bisa ka’ida ba shine domin a dakile matsalar rashin tsaro da mazauna yankin ke fuskanta
A cewar ministan rusau din zai habaka tsaftar birnin tarayya da kuma kawo cigaba
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya ba da umarnin ruguza shahararriyar kasuwar COVID-19 da ke Area 11, Abuja.
Daraktan Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB), Osi Braimah ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a lokacin da ake ruguza wasu shaguna da aka gina a kasuwar.