Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Malamar Jami’a
Al’ummar Jami’ar Jihar Nasarawa dake Keffi (NSUK) sun shiga cikin rudani yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da ɗaya daga cikin Malaman Jami’ar Dakta Comfort Adokwe.
Majiyarmu ta samu Rahoton cewa wasu ‘yan bindiga sun sace Adokwe, wato Malami a tsangayar sashen gudanarwar Mulki na Jami’ar kuma Mataimakin Daraktan nazarin jinsi a daren Lahadi a gidanta da ke Angwan Jaba a garin Keffi.
Shugaban kungiyar cigaban al’umma Kwamared Ali Sule wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ya ce ‘yan bindigar sun mamaye harabar Jami’ar ne da daddare, inda suka ɗauke ta suka garzaya da ita inda ba a san ko ina ne ba.
Ya ce masu garkuwan sun yi harbin iska da dama kafin daga bisani su tafi da Malamin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin Tsaro: Al’ummar Kaduna na nuna fargaba kan mamayar mayakan Ansaru
Ya kuma bayyana cewa “Gaskiya ne ‘yar uwarmu Dakta Comfort Adokwe, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da ita a daren jiya a gidanta da ke Angwan Jaba a garin Keffi.
Ya ƙara da cewar suna fatan tankasance cikin salama da fatan kuma za ta ya dawo mana lafiya.
Muna kira ga jami’an tsaro da su kai ɗauki domin a dawo da ita lafiya”.
Sai dai da wakilin mu ya tuntubi DSP Ramhan Nansel Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sandan Jihar, (PPRO), ya ce bai san da faruwar lamarin ba saboda ba a yi masa bayani ba.
Lamarin dai ya zo ne mako guda da sace daliban jami’ar kimanin hudu daga dakin kwanan su da ke kusa da Angwan Kare.
A wani labarin kuma:“Shirin lamunin Karatu ga dalibai zai fara aiki a watan Janairun 2024” – Tinubu
“Shirin lamunin Karatu ga dalibai zai fara aiki a watan Janairun 2024” – Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin ya bayyana cewa zamanin yajin aiki a Ƙungiyoyi keyi a cikin sha’anin ilimin kasar nan ya zo ƙarshe.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Jawabin da ya gabatar a wajen taron shekara-shekara na tattalin arzikin Najeriya karo na 29 wanda kungiyar tattalin arzikin Najeriya NESG ta shirya a Transcorp Hilton Abuja.
Tinubu ya kuma bayyana cewa shirin bayar da lamuni na daliban a gwamnatin sa zai fara ne a watan Janairun shekarar 2024.