- Dubban mahaddattan karatun AlQur’ani mai girma ne suka yi dandazo a cibiyar Cibiyar Bincike da Ci gaban Al’Qur’ani ta Majidadi don samun gurbin karatu
- Daliban sun ce an gaya mana cewa idan muka kammala lokacin karatun, za a ba mu damar yin karatu a kasashen waje
- Hakan ya kasance don ba su damar ci gaba da karatu na ilimi mai zurfi
Biyo bayan kaddamar da Cibiyar Bincike da Ci gaban Al’Qur’ani ta Majidadi da aka bude a bikin cikar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shekaru 67 da haihuwa, dubban mahaddattan karatun AlQur’ani mai girma ne suka yi dandazo a cibiyar domin neman gurbin karatu,Leadership ta rahoto.
Duk da cewa ’yan takara dari ne suka yi nasara da cika sharuddan shiga jami’ar ,za a karbe su a matsayin dalibai na farko a cibiyar, an ga matasa maza da mata sun yi jerin gwano da sanyin safiyar ranar Litinin yayin da wasu dubbai suka yi rajistar daukar aikin.
KARANTA WANNAN: Kotun Zaben Kano: Tsohon Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Wakilai Ya Doke Dan Takarar NNPP
Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a ranar bikin haihuwarsa ya ware wani bangare na gidansa da ke titin Miller Road domin kaddamar da wata cibiyar bincike ta addinin musulunci ta masu haddar Al-Qur’ani mai girma.
Daya daga cikin da’irar makarantar shi ne zabar wadanda suka haddace AlQur’ani gaba daya da koyar da su harsunan Ingilishi da Larabci da dai sauransu da kuma ba su takardar shedar makarantun firamare da sakandare da kuma ba su shaidar difloma a karshen kwas.
Wannan an yi niyya ne don ba su damar ci gaba da karatu na ilimi mai zurfi.
Wani yaro dan shekara 16 mai suna Ghali Murtala wanda a halin yanzu yana shekara ta biyu a daya daga cikin kananan makarantun gaba da sakandire a Kano ya ce ya haddace Al-Qur’ani kuma zai so ya yi amfani da damar da ya samu na yin karatu a cibiyar.
“An gaya mana cewa idan muka kammala lokacin karatun, za a ba mu damar yin karatu a kasashen waje,” in ji shi.
Khadeeja Abdullahi, ‘yar shekara 17, ta ce ta haddace Al-Qur’ani gaba dayansa, kuma tana son a ba ta takardar sheda domin ta samu damar shiga jami’a domin ci gaba da karatun ta.
“Ina nan tare da yayata domin a yi min rajista da fatan shigar da ni makarantar. Ina so in sami takadar sheda don kara ilimi da shiga jami’a. Ban sami damar zuwa makarantar sakandare ba,” in ji ta.
A wani labarin kuma,Tsohon Shugaban Kasa Ya Bada Shawarin Yadda Za a Gyara Ilimi
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya yi kira da a samar da isasshen jari a fannin ilimi domin gina al’umma ta gari
Idan masu kula da ilimi za su saka hannun jari a cikin ɗalibai, za a yi tasiri mai kyau ga ilimi
Ilimi na a matsayin ginshikin rayuwar yau da kullum da kuma kayan aikin ‘yantar da jama’a daga jahilci
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) ya yi kira da a samar da isasshen jari a fannin ilimi domin gina al’umma ta gari.
Gowon ya bayyana hakan ne a yayin bikin godiya da bikin cika shekaru 20 da kafa kwalejin kasa da kasa ta Africa a Abuja ranar Lahadi.