- Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) ta dauki wani muhimmin mataki na yaki da ta’addanci ta hanyar amincewa da daukar ‘yan banga guda 20
- Sace mutane abin damuwa ne ga mahukuntan jami’ar duk da cewa an san matsala ce ta kasa baki daya
- Hakan ya biyo bayan sace awon gaba da wasu dalibai da malaman makarantar tare da sakar su bayan an biya su kudin fansa
Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) ta dauki wani muhimmin mataki na yaki da ta’addanci ta hanyar amincewa da daukar ‘yan banga guda 20 da za a tura cikin dabara a wurare daban-daban da ba a cikin harabar jami’ar ba.
Farfesa Abdullahi Modibbo mataimakin shugaban jami’ar ta NSUK, ya bayyana a wata hira da manema labarai a kwanakin baya cewa jami’ar ta kuduri aniyar dakile matsalar garkuwa da mutane da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikata da dalibai.
KARANTA WANNAN: Sanata da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Fice Daga Jam’iyyar
“Sace mutane abin damuwa ne ga mahukuntan jami’ar duk da cewa mun san matsala ce ta kasa baki daya.
“Ga wadanda ke harabar jami’ar, ba mu da matsala sosai saboda muna aiki tare da hadin gwiwar jami’an tsaron Najeriya na Civil Defence.
“Ga wadanda ke wajen harabar jami’ar, mun amince da daukar ’yan banga guda 20 wadanda za a horar da su dabarun gudanar da ayyukansu a lungu da sako na wurare daban-daban a wajen harabar.
“Wannan na daya daga cikin kokarin da muke yi na tabbatar da tsaron ma’aikata da daliban,” in ji Modibo.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa a baya-bayan nan ne masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da wasu dalibai da malaman makarantar tare da sakar su bayan an biya su kudin fansa.
A kwanakin baya, Dakta Monica Adokwe, wata malama a tsangayar gudanarwa ta jami’ar, ta samu ‘yanci bayan an biya wadanda suka sace ta wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba.
A wani labarin kuma, Allah Ya Kusa Kubutar Da Najeriya – Gwamna PDP
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce Allah na gab da ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki
“Yana gab da sanya Najeriya tashi. Muna so mu gode wa Allah da abin da ya yi mana
Duk da cewa abubuwa sun yi wuya a yanzu, za mu iya samun sauki da yardar Allah
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a ranar Lahadi ya ce Allah na gab da ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wani gangamin yakin neman zabe da Cocin Deeper Life ta shirya a birnin Benin, babban birnin jihar.