- Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ce gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ba ta da alhakin tsare Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB
- “Hanya ta daban” ba za ta fito fili ba har sai ta samar da sakamakon da ake bukata
- Sabuwar gwamnati ba ta bukatar ta gaji munanan ayyukan gwamnatin da ta gabata
Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ce gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ba ta da alhakin tsare Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB).
Otti ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tukuru don ganin an sako Kanu.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kano Za ta Biya N6bn Ga Ma’aikatan da Suka Yi Ritaya
Ya ce gwamnatinsa ta bullo da “hanya ta daban” don ganin an sako Kanu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Umuahia, babban birnin jihar.
Otti ya ce “hanya ta daban” ba za ta fito fili ba har sai ta samar da sakamakon da ake bukata.
Ya yi nuni da cewa ya na aiki a karkashin kasa don ganin an sako shugaban na IPOB duk da bai bayyana kokarinsa ga manema labarai ba.
“Na yi imani da sakamako yada labarai. Ba ma son hayaniyar kafofin watsa labarai. Muna aiki tukuru don ganin an sako shi (Kanu),” inji shi.
Gwamnan ya ce gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ba ta da alhakin tsare Kanu.
“Matsayina shi ne, sabuwar gwamnati ba ta bukatar ta gaji munanan ayyukan gwamnatin da ta gabata,” inji shi.
A wani labarin kuma, FEC ta Amince da Naira Tiriliyan 2.1 Na Karin Kasafin Kudin 2023
Majalisar zartarwa ta tarayya FEC ta amince da karin kasafin kudi na sama da Naira tiriliyan N2.1 don tallafawa al’amuran kasa
Ministan Kasafin Kudi da Tsaren Tattalin Arziki ne ya bayyana hakan a karshen taron FEC
Majalisar ta amince da Naira biliyan 605 ga fannin tsaro
Majalisar zartarwa ta tarayya FEC a ranar Litinin ta amince da karin kasafin kudi na Naira tiriliyan N2,176,791,286,033 don tallafawa al’amuran kasa na gaggawa da suka hada da Naira biliyan 605 na tsaro.
Ministan Kasafin Kudi da Tsaren Tattalin Arziki Sanata Abubakar Bagudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati a karshen taron FEC a Abuja.