- Shugaba Bola Tinubu ya shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da ya kawo karshen burinsa na neman mulkin Najeriya
- Najeriya na ci gaba don cimma kaddararta, amma burin Atiku na neman shugaban kasa ya lalace
- Bacin ran Atiku kan dimokuradiyyar mu, muna jin dadin gaya wa duniya cewa dimokuradiyyar mu tana ci gaba da bunkasa
Shugaba Bola Tinubu ya shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da ya kawo karshen burinsa na neman mulkin Najeriya, Daily Post ta rawaito.
Now is time to end your presidential ambition – Tinubu replies Atiku
Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin da yake murza ikirari na Atiku na cewa Najeriya ta lalace bayan hukuncin kotun koli da ta yi watsi da karar da ya shigar.
KARANTA WANNAN: Muna Aiki Tukuru Don Ganin An Sakin Nnamdi Kanu – Gwamna Otti
Ya ce Najeriya ta na ci gaba don cimma kaddararta, amma burin Atiku na shugaban kasa ya lalace.
A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ya fitar, Tinubu ya ce: “Muna so mu gaya wa Alhaji Atiku wannan: Najeriya ba ta halaka ba. Mummunan burin Atiku na zama Shugaban kasa ne kawai ya lalace.
“Najeriya na ci gaba da shirin cimma kyakkyawar makoma a matsayinta na daya daga cikin kasashen duniya da ake mutuntawa da samun nasara a karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Sabanin bacin ran Atiku kan dimokuradiyyar mu, muna jin dadin gaya wa duniya cewa dimokuradiyyar mu tana ci gaba da bunkasa.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa, a karon farko tun shekarar 1999, halayen Majalisarmu ta kasa da yadda take nuna bambancin zabi da zabin masu kada kuri’a a matsayin hadakar bakan gizo na jam’iyyu daban-daban, sabanin yadda ake yi a baya . jam’iyyu biyu ne suka mamaye majalisar dokokin kasar.
“A Najeriya ta yau, an kirga kuri’u. Babu wani murguda gaskiya da gangan kan zabenmu na baya-bayan nan da Alhaji Atiku da takwaransa, Peter Obi, zai iya haifar da ci gaba da inganta harkokin zabenmu, wanda masu sa ido na gida da waje suka yaba.
“Kamar yadda Kotun Koli ta ayyana, IReV ba a tsara ta azaman cibiyar tattara sakamakon zaben yanar gizo ba. Sai kawai cibiyar kallon jama’a don sakamako.
“Muna so mu ba Atiku shawara cewa bayan shafe shekaru 30 yana neman shugabancin Najeriya, dole ne ya kawo karshen yunkurinsa na rashin fa’ida, ya daina duk wani aiki da zai kara gurbata yanayin siyasa da zaman lafiyar kasa.”
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Za ta Biya N6bn Ga Ma’aikatan da Suka Yi Ritaya
Gwamnatin Kano na shirin biyan Naira biliyan 6 a matsayin giratuti ga ma’aikatan gwamnati kusan 5,500
Asusun na daga cikin abin da aka ware domin biyan sama da Naira biliyan 40 na kudaden da suke bin gwamnatin da ta shude
Kullum ina kwana ina farkawa da batun giratutin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a raina
Gwamnatin jihar Kano na shirin biyan Naira biliyan 6 a matsayin giratuti ga ma’aikatan gwamnati kusan 5,500 da suka yi ritaya.
Abba Yusuf, gwamnan jihar Kano ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar.