- Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana shirinta na gudanar da sahihin zaben gwamna da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba, 2023 a jihar Imo
- Duk hukumomin tsaro sun bayar da tabbacin zaben ba zai haifar da wata matsala da cin zarafi ba
- Za a gudanar da zabe a rumfunan zabe 4,750 a fadin jihar, sai dai a rumfunan zabe 38 ba za a yi zabe ba
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana shirinta na gudanar da sahihin zaben gwamna da aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 a jihar Imo.
Kwamishiniyar zabe ta jihar Imo, Farfesa Sylvia Agu ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a ranar Laraba a hedikwatar INEC da ke Owerri.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Masu Zanga-zanga Sun Mamaye Majalisar Dattawa, Sun Bukaci a Kori Ministan Tsaro
Ta ce hukumar ta kammala ayyuka 11 da suka shafi zaben ranar 11 ga watan Nuwamba daga cikin 13, inda ta bada tabbacin kammala sauran ayyuka 2 kafin zaben.
Agu ta ce, ba wai kawai hukumar ta gudanar da dukkan ayyukan da aka yi kafin zaben cikin wa’adin lokaci ba, har ma ta gudanar da tarurruka da masu ruwa da tsaki da suka hada da jam’iyyun siyasa, sarakunan gargajiya, kungiyoyin farar hula, shugabannin kafafen yada labarai, da ‘yan jarida, domin cimma matsayar dabarun da za su taimaka wajen gudanar da zabe mafi inganci da adalci a jihar
Ta kuma ba da tabbacin fara tafiya da kuma isowar kayayyakin zabe zuwa dukkan cibiyoyin zabe a jihar, tare da ba da hadin gwiwar da suka dace da hukumomin sufuri a jihar.
Ta ce, “Da Misalin karfe 8.30 na safe, an kwashe duk kayan zuwa cibiyoyin.”
Farfesa Agu ta bayyana cewa ya zuwa yanzu masu kada kuri’a sun karbi katin zabe guda 318,919 a jihar, yayin da har yanzu ba a gama karban PVC guda 101,003 ba.
REC din ta bada tabbacin cewa za a gudanar da zabe a rumfunan zabe 4,750 a fadin jihar, sai dai a rumfunan zabe 38, inda ba za a yi zabe ba.
Dangane da batun tsaro kuwa, REC ta bada tabbacin cewa, idan aka yi la’akari da duk tabbacin da hukumomin tsaro suka bayar a jihar, zaben ba zai haifar da wata matsala da cin zarafi ba.
A wani labarin kuma, Majalisar Dattawa ta Tabbatar Da Sunayen RECs na INEC Wadanda Tinubu Ya Nada
Majalisar dattawa ta wanke tare da tabbatar da jerin sunayen kwamishinonin INEC goma da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada
Shugaban Majalisar Dattawa shine wanda ya karanta wasikar ta Shugaba Tinubu na neman a tantance wadanda aka zaba
Tuni majalisar ta wanke sabbin kwamishinon wadanda aka aike mata
Yanzu haka dai majalisar dattawa ta wanke tare da tabbatar da jerin sunayen kwamishinonin INEC goma da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada kuma ya aike wa majalisar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta wasikar ta Shugaba Tinubu na neman a tantance wadanda aka zaba a zauren majalisar ranar Talata.