- Tsohuwar tauraruwar BBNaija, Uriel ta ce ta ji kamar ta bata damarta bayan fitar ta daga fitowar All-Stars
- Uriel ta fafata a kakar gasar shekarar 2017 ta BBNaija da kuma All-Stars da aka kammala kwanan nan
- An kore ta bayan makonni 3 kacal a lokacin damarta ta biyu a gasar
Tsohuwar tauraruwar BBNaija, Uriel ta ce ta ji kamar ta bata damarta bayan fitar ta daga fitowar All-Stars da aka kammala kwanan nan.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa Uriel ta fafata a kakar gasar shekarar 2017 ta BBNaija da kuma All-Stars da aka kammala kwanan nan.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta Fara Gina Gidajen Tsugunar da ‘Yan Gudun Hijira
An kore ta bayan makonni 3 kacal a lokacin damarta ta biyu akan wasan kwaikwayo na gaskiya.
Da take magana a ranar Alhamis, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, Uriel ta bayyana yadda ta ji bayan fitar ta karo na biyu
Ta rubuta: “Na bar All-stars ina jin kamar na lalata damata. Makonni 3 akan nunin. Amma Allah yace Uubeekee sati 3 shine abinda kuke bukata.
“Naji Allah ya bani sa’a. Allah ya kyauta.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Isra’ila Ta Amince da Tsagaita Wuta Na Wasu Sa’o’i a Zirin Gaza – Fadar White House
Yanzu haka dai kasar Isra’ila ta amince da aiwatar da tsagaita bude wuta na tsawon sa’o’i hudu a kowace rana a yankin arewacin Zirin Gaza a cewar fadar White House
Tuni dai wannan sanarwa ta fara aiki nan take
A ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, rikici dauke da makamai ya barke tsakanin Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa karkashin jagorancin Hamas
Kusan wata guda bayan fara wani kazamin yaki tsakanin sojojin Isra’ila da mayakan Hamas, Isra’ila ta amince da aiwatar da tsagaita bude wuta na tsawon sa’o’i hudu a kowace rana a yankin arewacin Gaza, in ji fadar White House.
Kakakin Majalisar Tsaro na Fadar White House John Kirby ya ce za a ba da sanarwar sa’o’i uku kafin nan.