- Kwamishinan Ilimi na Jihar Yobe, Dr Muhammad Sani Idriss, ya karbi rahoto daga wani kwamitin wucin gadi da ya tantance matsayi da kuma bin manufofin dukkan makarantu masu zaman kansu na jihar
- Bai kamata makarantu masu zaman kansu a jihar su fifita samun kudi fiye da nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da ingantaccen ilimi ba
- Duk wata makaranta mai zaman kanta da ta ki bin wadannan sharudda to gwamnati za ta garkame ta
Kwamishinan Ilimi a matakin farko da Sakandare na Jihar Yobe, Dr Muhammad Sani Idriss, ya karbi rahoto a ranar Alhamis daga wani kwamitin wucin gadi da ya tantance matsayi da kuma bin manufofin dukkan makarantu masu zaman kansu na jihar.
Da yake karbar rahoton kwamitin da shugaban kwamitin, Dokta Abba Idriss Adam ya gabatar masa, kwamishinan ya jaddada cewa bai kamata dukkan makarantu masu zaman kansu su kauce wa al’adu, ka’idoji, da kimar al’ummar jihar ba.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Imo Ya Magantu Kan Farmakin da Aka Kaiwa Shugaban NLC Ajaero
Ya kara da cewa, bai kamata makarantu masu zaman kansu a jihar su fifita samun kudi fiye da nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da ingantaccen ilimi ba.
“Dukkanin makarantu masu zaman kansu a jihar su ma su bi manufofi da tsare-tsare na gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni wajen bunkasa fannin ilimi a jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ya nanata matsayin ma’aikatar cewa duk wata makaranta mai zaman kanta da ta ki bin wadannan sharudda to gwamnati za ta rufe ta.
Haka kuma ya yi kira ga masu mallakar makarantu masu zaman kansu da ba su yi rajista da ma’aikatar ba da su yi hakan da kuma wadanda suka rigaya suka yi rajista da su nemi sabunta lasisi kafin watan Disamba 2023.
Dr Idriss ya yi gargadin cewa gwamnati a jihar ba za ta lamunci kutsawa cikin littattafan da ba a so ba.
“A Jihar Yobe, muna daraja imaninmu da al’adunmu kuma muna ba da fifiko ga ɗabi’a. Don haka, za mu kiyaye su da kishi da kuma hana mugayen al’adu su lalata su,” inji shi.
A wani labarin kuma, Simeone Ya Tsawaita Kwantiraginsa da Atletico
Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya sanya hannu kan tsawaita kwantiragin na tsawon shekaru uku har zuwa watan Yunin shekarar 2027
Ya kasance tsohon dan wasan tsakiya ne a kungiyar, ya taba horar da kungiyar a wasanni mafi yawa a tarihinta inda ya lashe kofuna takwas
A halin yanzu kulob din yana matsayi na hudu a teburin gasar La Liga
Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya sanya hannu kan tsawaita kwantiragin na tsawon shekaru uku har zuwa watan Yunin shekarar 2027, in ji kulob din na Spain a ranar Alhamis.
Simeone, mai shekaru 53, wanda aka nada a watan Disambar shekarar 2011 “zai ci gaba da zama kocin kungiyarmu har zuwa 30 ga watan Yuni 2027”, in ji kungiyar a cikin wata sanarwa.