- Shugaban karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi, Muhammed Danasabe ya rasu
- Shugaban karamar hukumar ya rasu ne bayan wata gajeriyar rashin lafiya
- Mutuwar sa ta zo ne sa’o’i 24 kafin gudanar da zaben gwamna a jihar
Shugaban karamar hukumar Lokoja a jihar Kogi, Muhammed Danasabe ya rasu, Punch ta rawaito.
Danasabe ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a a wani asibitin Lokoja a wata gajeriyar rashin lafiya.
KARANTA WANNAN: Gwamna Makinde Ya Amince da Nadin Shugaban PDP a matsayin basaraken Gargajiya
Mutuwar sa ta zo ne sa’o’i 24 kafin gudanar da zaben gwamna a jihar.
A cewar wata majiya mai tushe, za a yi jana’izar marigayin a makabartar Musulmi ta Unguwan Kura bayan sallar Juma’a.
Ya rasu ya bar mahaifiyarsa, matarsa da ’ya’yansa.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Yobe Ta Karbi Rahoton Bin Manufofin Makarantu Masu Zaman Kansu
Kwamishinan Ilimi na Jihar Yobe, Dr Muhammad Sani Idriss, ya karbi rahoto daga wani kwamitin wucin gadi da ya tantance matsayi da kuma bin manufofin dukkan makarantu masu zaman kansu na jihar
Bai kamata makarantu masu zaman kansu a jihar su fifita samun kudi fiye da nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da ingantaccen ilimi ba
Duk wata makaranta mai zaman kanta da ta ki bin wadannan sharudda to gwamnati za ta garkame ta
Kwamishinan Ilimi a matakin farko da Sakandare na Jihar Yobe, Dr Muhammad Sani Idriss, ya karbi rahoto a ranar Alhamis daga wani kwamitin wucin gadi da ya tantance matsayi da kuma bin manufofin dukkan makarantu masu zaman kansu na jihar.
Da yake karbar rahoton kwamitin da shugaban kwamitin, Dokta Abba Idriss Adam ya gabatar masa, kwamishinan ya jaddada cewa bai kamata dukkan makarantu masu zaman kansu su kauce wa al’adu, ka’idoji, da kimar al’ummar jihar ba.