- Jami’an Hukumar EFCC sun kama wasu mutane 14 da ake zargi da sayen kuri’u a filayen zabe da kuma rumfunan zabe daban-daban
- An cafke wadanda ake zargin ne a wani samame da aka yi ta hanyar leken asiri
- Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC sun kama wasu mutane 14 da ake zargi da sayan kuri’u a filayen zaben Otueke, Adawari a Bayelsa da kuma rumfunan zabe daban-daban a Imo da Kogi, Daily Trust ta rawaito.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale shi ne wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.
KARANTA WANNAN: Mummunar Gobara Ta Lalata Shaguna 17 a Wata Kasuwa
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar Asabar a wani samame da aka yi ta hanyar leken asiri da aka fara kwanaki kadan gabanin zaben gwamnoni da ake gudanarwa a jihohin uku.
“Haka zalika, an kwato jimillar kudi Naira miliyan N11,040,000, wanda ya kunshi N9,310,00 da aka kama daga hannun wadanda ake zargin masu saye da sayarwa a Bayelsa, da kuma Naira miliyan N1,730,000 da aka kama daga hannun wadanda ake zargi da magudin zabe a fadin jihar Imo.
“Haka kuma an kama motoci biyu daga hannun wadanda ake zargin. Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike,” inji shi.
A wani labarin kuma, Zaben Imo: Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Koka Kan Sayen Kuri’u, Da Sauran Munanan Ayyuka
Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Imo,Sanata Samuel Anyanwu ya koka kan wasu kura-kurai da ake zargin an yi a zaben
Dan takarar yi kira da a soke sakamakon zaben a yankunan da ake zargin ‘yan daba sun haifar da tashe-tashen hankula
Ya kamata INEC ta yi la’akari da shaidun da ake da su tare da soke sakamakon zabe a yankunan da abin ya shafa
Sanata Samuel Anyanwu, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Imo, ya koka kan wasu kura-kurai da ake zargin an yi a zaben na ranar Asabar.
A yayin da yake magana kan rahotannin wakilan jam’iyyar na wuraren zabe, Anyanwu ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai a wasu rumfunan zabe da suka hada da sace akwatin zabe, sayen kuri’u da dai sauransu.