- Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan halartar taron Saudiyya da Afirka a makon jiya da kuma bikin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai na Guinea Bissau
- A ranar 9 ga watan Nuwamba ne shugaba Tinubu ya bar Abuja domin halartar wani muhimmin taro a kasar Saudiyya
- Shugaban Guinea-Bissau Embalo a bikin cikar kasar shekaru 50 ya ce kasar ta samu ci gaba ta hanyar karfafa dangantakarta da sauran kasashe
Shugaban kasa Bola Tinubu a yammacin ranar Alhamis ya dawo Najeriya bayan halartar taron Saudiyya da Afirka a makon jiya da kuma bikin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai na Guinea Bissau a ranar Alhamis.
A ranar 9 ga watan Nuwamba ne shugaba Tinubu ya bar Abuja domin halartar taron Saudiyya da Afirka da aka yi a birnin Riyadh wanda ya hada da kara jawo jarin kasashen waje kai tsaye da kuma fadada huldar kasuwanci.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Kano
Gwamnatin Wata Jiha Ta Dakatar da Basaraken Gargajiya Kan Wani Zargi
Tattaunawar da aka yi a taron koli na farko na Saudiyya da Afirka ya ta’allaka ne kan tallafawa ayyukan hadin gwiwa, da inganta hadin gwiwar siyasa, da magance barazanar tsaro a yankin, da samar da sauye-sauyen tattalin arziki ta hanyar bincike.
Kazalika tattaunawar ta hada da samar da sabbin hanyoyin samar da makamashi a cikin gida, tare da karfafa hadin gwiwar zuba jari tsakanin bangarori daban daban.
A daren Laraba ne shugaba Tinubu ya bar kasar Saudiyya inda ya isa kasar Guinea Bissau da sanyin safiyar Alhamis domin karrama goron gayyatar da shugaban kasar ya yi masa na bikin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai.
Shugaban wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, ya bi sahun shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Azaali Assoumani da wasu shugabannin kasashe biyar a wajen bikin da aka baje kolin tarihi, al’adu da sojoji.
Shugaban kasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo ya godewa dukkan shugabannin bisa karrama wannan gayyata, musamman abokan huldar da suka tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar, kamar Najeriya.
Da ya waiwayi shekaru 50 da samun ‘yancin kai, Embalo ya ce kasar ta samu ci gaba ta hanyar karfafa dangantakarta da sauran kasashe, yana mai ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dore, tare da inganta dangantakar tattalin arziki da jin kai.
Sauran shugabannin da suka halarci bikin sun hada da Dennis Sassou N’Guesso, shugaban Congo, Brice Clotaire Engeuma, shugaban rikon kwarya na Gabon, Adama Barrow, shugaban Gambia, Marcelo Rebelo de Sousa, shugaban kasar Portugal, da Julius Maada Bio na kasar. Saliyo.
Shugaba Tinubu dai ya bar Bissau ne bayan an kammala bikin zuwa Najeriya da misalin karfe 4 na yamma.
A wani labarin kuma, PDP ta Kaddamar da Jaddawalin Zaben Gwamnan Jihar Edo
Jam’iyyar PDP a hukumance ta bayyana jaddawalin da zasu jagoranci gudanar da wasu ayyuka tun kafin zaben gwamnan Edo
Tuni jam’iyyar PDP ta bayyana lokacin da za a gudanar da taron tantance dan takarar gwamna jihar
Dole ne duk wani dan takarar da ke neman wannan mukami da su samu fom din tsayawa takara a kan Naira miliyan 21
Jam’iyyar PDP a hukumance ta bayyana jaddawalin da zasu jagoranci gudanar da wasu ayyuka tun kafin zaben gwamnan jihar Edo.
Kwamitin gudanarwa na kasa ne ya fitar da jadawalin a ranar Alhamis bayan wani taron hadin gwiwa na kwamitin amintattu da kwamitin zartarwa na kasa a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.