- ‘Yan wasan kasar Zimbabwe sun koma atisaye bayan sun janye yajin aikin da suka tsunduma na kwana daya
- ‘Yan wasan sun tsunduma yajin aikinne bayan wata ta kaddama da hukumar kwallon kafar kasar
- Tuni hukumar kwallon kafar kasar ta shiga ta fita don ganin an warware takunsakar
‘Yan wasan kasar Zimbabwe sun koma atisaye a ranar Juma’a (Yau) bayan sun janye yajin aikin da suka tsunduma na kwana daya.
‘Yan wasan sun ki yin atisaye a ranar Alhamis yayin da suke nuna rashin amincewarsu da rashin biyan su alawus-alawus da kuma kudaden shiga.
KARANTA WANNAN: Kano: Kar Ka Je Kotun Koli, Ka Jira Har zuwa 2027 – Kwankwaso Ga Gwamna Abba Gida-gida
Warriors sun yi kunnen doki 0-0 a gasar cin kofin duniya na FIFA 2026 a ranar Laraba.
Sun kuma bukaci a ba su alawus daga wasan duk da cewa hukumar kwallon kafa ta Zimbabwe (ZiFA) ta yi tanadin wani kari ne kawai.
A cewar Herald, sai da ZiFA ta zagaya domin tabbatar da cewa sun saka kudaden a asusun ‘yan wasan da yammacin jiya domin dakile wata takun-saka tsakanin su da Najeriya.
Tawagar Baltemar Brito za ta karbi bakuncin Super Eagles a filin wasa na Huye, Butare, ranar Lahadi.
A wani labarin kuma, Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Yabawa Hukuncin Kotun Daukaka Kara
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Abdulkadir ya yaba da nasarar da ya samu a kotun daukaka kara a zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar watan Maris 2023
Gwamnan ya bayyana cewa, “Wannan wata shaida ce ta jajircewata na ba da gudummawar dimokuradiyya ga ‘yan kasa”
Gwamnan ya yi kira ga jam’iyyun adawa a jihar da su hada kai su marawa shirin manufofin gwamnatinsa baya
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ya yaba da nasarar da ya samu a kotun daukaka kara a zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
A cikin tabbataccen shafin sa na dandalin sada zumunta, Gwamnan ya bayyana cewa, “Wannan wata shaida ce ta jajircewata na ba da gudummawar dimokuradiyya ga ‘yan kasa.”