Cibiyar horas da sojoji ta Najeriya (NDA) ta ce za ta gudanar da atisayen harbi na shekara-shekara da kuma horas da harbe-harbe ga Cadets na 73 Regular Course kuma ta bukaci mazauna yankin da kada su firgita.
Jami’in hulda da jama’a na makarantar, Manjo Mohammed Maidawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Kaduna.
Karanta nanKano: Kar Ka Je Kotun Koli, Ka Jira Har zuwa 2027 – Kwankwaso Ga Gwamna Abba Gida-gida
Hukumar NDA na son sanar da jama’a, musamman mazauna yankunan Mando, Tsamiya, Kauya, da Afaka, cewa za ta gudanar da ayyukanta na koyon harbin bindiga na shekara-shekara na ma’aikatan NDA na rundunar sojojin Nijeriya (NA) da NDA.
Ya bayyana cewa an shirya gudanar da atisayen ne tsakanin ranakun 20 zuwa 30 ga watan Nuwamba a NDA Open Range Afaka.
Maidawa ya tabbatar wa jama’a cewa an samar da dukkan matakan tsaro domin samun nasarar gudanar da atisayen.
Sai dai ya shawarci jama’a da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su da su guji gifatawa ta wajen a duk tsawon lokacin da ake gudanar da atisayen. (NAN.
A wani labarin kuma
Gwamna Sule Ya Bukaci Hukumar WAEC Ta Hana Satar Jarabawa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi kira ga hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Najeriya (WAEC) da ta dauki matakin rage yawaitar tabarbarewar jarabawa.
Sule ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Lafiya a taron shekara-shekara na NNC na WAEC karo na 61.
Ya lura cewa don kawar da irin wannan kuskuren sosai akwai bukatar daukar matakan ladabtarwa ga duk wanda aka samu da laifin satar amsa.
Ya ce, domin kare makomar yara da kuma makomar kasa baki daya, akwai bukatar a gaggauta magance matsalar jarabawa domin ta kasance babbar matsala ga harkar ilimi