- Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dawo da martabar ilimi a jihar
- Gwamnatin jihar na baiwa ilimi fifiko domin cika alkawuran yakin neman zabe da Gwamnan ya dauka
- Tuni Gwamnati ta fara aikin ginawa da kuma gyara makarantu 245 a fadin kananan hukumomi 14 da ke jihar
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dawo da martabar ilimi a jihar, Daily Trust ta rahoto.
Da yake bayar da tabbacin a wajen kaddamar da fara gine-gine da gyaran makarantu a hukumance, Gwamna Lawal ya jaddada kudirinsa na farfado da ilimi.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta Soke Lasisin Kamfanonin Hakar Ma’adanai Sama da 1k
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamnatin jihar na baiwa ilimi fifiko domin cika alkawuran yakin neman zabe.
A cewarsa, fara ayyukan ya yi daidai da dokar ta-baci da aka ayyana a fannin ilimi.
Ya ce: “Lokacin da ake gabatar da wasikun bayar da lambar yabo ta gine-gine da gyara makarantu a Jihar Zamfara, Gwamna Lawal ya bayyana kudirinsa na inganta fannin ilimi gaba daya.
“Aikin kaddamar da tuta na ginawa da gyara ajujuwa ne, da kayayyakin WASH, katangar makaranta, da samar da kayan daki ga dalibai da malamai a makarantunmu, duk a cikin tsarin dokar ta-baci da gwamnati ta ayyana.
“Shahararrun ‘yan kwangilar ‘yan asalin kasar ne za su gudanar da ayyukan. Ayyukan sun hada da sake gyara makarantun da suka lalace gaba daya a fadin kananan hukumomin 14. Wannan baya ga sabbi, da suka hada da makarantun Tsangaya dake shiyyar uku na Anka, Kaura Namoda, da Gusau.
“Domin aiwatar da wadannan ayyuka, Jimillar Naira biliyan hudu da miliyan dari uku da arba’in da shida da dari hudu da dubu hamsin da dari biyu da Tara da kobo 19 Kobo kacal (4,346,450,209.19) gwamnati ta ware.
“An zaɓi ƴan kwangilar aikin a tsanake bisa amincinsu da gogewarsu wajen tafiyar da ayyuka iri ɗaya.
“Aikin ya kunshi ginawa da kuma gyara makarantu 245 a fadin kananan hukumomi 14 da ke jihar. Bugu da kari, za a samar da tebura masu kujeru biyu guda 9,542 ga dalibai a makarantu a fadin kananan hukumomin 14.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Filato ta Samu Sabon Kakakin Majalisa da Mataimaki
Kakakin majalisar dokokin Filato, Moses Thomas Sule da mataimakinsa, Hon Gwottaon sun yi murabus daga mukamansu
Hakan ya faru ne yayin da majalisar ta zabi sabon kakakin majalisa
Kawo yanzu Babu cikakken Bayani kan murabus din tsohon Kakakin Majalisar da mataimakinsa
Kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Moses Thomas Sule da mataimakinsa, Hon Gwottaon sun yi murabus daga mukamansu.
Hakan ya faru ne yayin da majalisar ta zabi dan majalisa mai wakiltar Pankshin ta Arewa, Gabriel Dawang, a matsayin sabon kakakin majalisar.