- Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong na shirin yin murabus Daga mukaminsa na Minista
- Tuni ministan ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC
- Kafin daukar wannan matakin a baya kotun daukaka kara ta kori Dan takarar PDP tare da bayyana ministan na Tinubu a matsayin Sanata
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong na shirin yin murabus Daga mukaminsa, Daily Post ta rahoto.
Ministan ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano Yusuf ya Garzaya Kotun Koli Kan Hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta Yanke
A baya kotun daukaka kara ta kori Bali Napoleon na jam’iyyar PDP tare da bayyana Lalong a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta Kudu.
A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Osun Ta Jaddada Aniyarta Na Dakatar da Babban Alkalin Alkalan Jihar
Majalisar dokokin Osun ta sake jaddada aniyar ta na kawar da bangaren shari’a daga cikin halin da take ciki na cin hanci da rashawa
Majalisar tayi watsi da cewa ba gaskiya ba ne cewa matakan da aka dauka kan CJ na da nasaba da muradun siyasa
Kafin Hakan dai mambobin Kungiyar Ma’aikatan Shari’a Ta Jihar sun Ayyana tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Majalisar dokokin jihar Osun ta sake jaddada aniyar ta na kawar da bangaren shari’a daga cikin halin da take ciki na cin hanci da rashawa.
Majalisar ta kuma jaddada cewa kudurin da ta yanke kan babban alkalin alkalai na jihar, Mai shari’a Oyebola Adepele Ojo, na janye shi daga gefe ya yi daidai da tsarin gaskiya da adalci.