- Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana bayar da kujerun aikin Hajji ga daukacin wadanda suka yi nasara a gasar karatun Al-Qur’ani da ake yi a jihar
- Tuni dai wadanda suka lashe gasar daga matsayi na daya zuwa na hudu a bangarori daban-daban suka rabuta da kyauta tsabar kudade
- Al-Qur’ani shi ne mafita wajen kawo karshen kalubalen ta’addanci domin duk wanda ya fahimci Al-Qur’ani ba zai shiga ta’addanci da fashi ba
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana bayar da kujerun aikin Hajji ga daukacin wadanda suka yi nasara a gasar karatun Al-Qur’ani da ake yi a jihar a bangaren maza da mata.
A cewar gwamnan, wadanda suka yi nasara biyu za su kasance cikin malaman da za su zama jagora da wa’azi ga maniyyatan jihar a lokacin aikin Hajjin 2024.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: ‘Yan majalisar Dokokin Ondo Sun Shiga Ganawar Sirri, Za su Iya ayyana Sabon Mukaddashin Gwamna
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen kammala gasar karatun Al-Qur’ani ta shekara wanda aka gudanar a Kaduna, babban birnin jihar ranar Asabar.
Ya kuma bayar da kyautar kudi ga wadanda suka lashe gasar daga matsayi na daya zuwa na hudu a bangarori daban-daban.
Sani, yayin da yake magana kan aikin Hajji na shekarar 2024, ya ce ya kaddamar da wani kwamiti don tabbatar da cewa aikin Hajji na gaba bai fuskanci wani cikas da kuma wani babban ci gaba a aikin na 2023 mai dauke da kalubalen wurin kwana da ciyarwa ba.
Yayin da yake lura da cewa mutane da yawa sun tuntube shi don neman kwangilar ayyukan Hajji kamar kayan aikin Hajji, abinci da wurin kwana da sauransu, gwamnan ya ce.
“Abin da nake so na gaya wa duk wanda ya samu kwangilar aikin Hajji, shi ne ya ji tsoron Allah, kuma ya bai wa alhazai abin da ya dace domin su samu addu’o’in alhazai, ba fushin Allah da alhazai za su yi hidima ba. ” in ji shi.
A halin da ake ciki, Jagoran kungiyar Jama’atu Izalatu Bid’ah Wa Ikamatu Sunnah ta kasa, Abdullahi Lau, a lokacin da yake gabatar da lacca a wajen taron, ya kuma ce Al-Qur’ani shi ne mafita wajen kawo karshen kalubalen ta’addanci domin duk wanda ya fahimci Al-Qur’ani ba zai shiga ta’addanci da ‘yan fashi ba.
Ya bukaci malaman musulunci da su koma ga Al-Qur’ani mai girma don tabbatar da cewa zaman lafiya ya yi mulki, yana mai cewa hakan ne kawai mafita ga kalubalen tsaro da ke addabar kasar.
Malamin addinin musuluncin wanda ya yabawa gwamnan bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen yada addinin musulunci ya bukace shi da ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri na tsohon gwamna Nasir El-Rufai.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya musamman al’ummar musulmi da su nisanci bautar wanin mahaliccinsu.
Shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Dahiru Liman, ya kuma sanar da bayar da gudunmuwar kudi naira miliyan 1.5 ga wadanda suka yi nasara da kuma alkalan gasar.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara ta Tabbatar da Zaben Abiodun, Ta Bada Umarnin Sake Sabon Zabe
Kotun daukaka kara da ke Legas a wani hukunci da ta yanke, ta tabbatar da sake zaben Prince Dapo Abiodun a matsayin zababben gwamnan Ogun
Alkalin kotun ya yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP ya shigar na kalubalantar Nasarar Abiodun
Sai dai bayan Yanke Hukuncin Alkalin kotun ta bayar da umarnin sake sabon Zabe
Kotun daukaka kara da ke Legas a ranar Juma’a a wani hukunci da ta yanke, ta tabbatar da sake zaben Prince Dapo Abiodun a zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023 a matsayin zababben gwamnan Ogun.
Hukuncin mafi rinjaye da mai shari’a Joseph Shagbaor Ikyegh ya yanke ya yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu ya shigar a zaben gwamna na 2023.