- Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan Sokoto
- Jam’iyyar PDP da dan takararta, sun tunkari kotun daukaka suna kalubalantar nasarar APC da dan takararta a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris
- Tunda farko kotun zaben gwamna ta tabbatar da nasarar Aliyu na jam’iyyar APC a wani hukunci da ta yanke
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Sokoto
Wasu alkalai uku na kotun sun tabbatar da Aliyu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris bayan da ya yi watsi da daukaka karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar ya shigar.
KARANTA WANNAN: Dimokuradiyyar Kasashen Turai Ba Ta Yi Kasa a Gwiwa Ba a Najeriya — Tsohon Minista ga Obasanjo
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zamanta a Jos, jihar Sokoto ta tabbatar da nasarar Aliyu na jam’iyyar APC a wani hukunci da ta yanke tun da farko.
Kotun ta yanke hukuncin cewa wadanda suka shigar da karar, PDP da dan takararta, sun kasa tabbatar da hujjar su ba tare da wata shakka ba.
Jam’iyyar PDP da dan takararta, Sa’idu Umar, sun tunkari kotun suna kalubalantar nasarar APC da dan takararta, Ahmad Aliyu, a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Sun mika neman adalci ga kotun daukaka kara inda su ma suka yi rashin nasara a ranar Litinin.
A wani labarin kuma, Fasinjoji Sun Firgita, Bayan Wani Jirgi Ya Sauya Wajen Sauka
Wani jirgin saman United Nigeria Airline NUA0504 da ke aiki daga filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas kan hanyarsa ta zuwa Abuja ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Asaba
Ma’aikatan jirgin sun yi wata sanarwa ba daidai ba lokacin da suka sauka lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin fasinjojin
Lamarin dai ya faru me bisa dalilai na yanayi
Wani jirgin saman United Nigeria Airline NUA0504 da ke aiki daga filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas kan hanyarsa ta zuwa Abuja ranar Lahadi ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Asaba da ke jihar Delta.
Wannan ci gaban, wanda ya zama kamar ya girgiza fasinjojin, an ce ya faru ne saboda rashin kyawun yanayi a babban birnin kasar Abuja.