- Jam’iyyar SDP, a jihar Kogi, ta bukaci da a gaggauta mayar da kayayyakin hukumar INEC Masu motsi zuwa Abuja
- Ba abin yarda ba ne a samu wasu mutane masu alaka ta kut-da-kut da manyan masu ruwa da tsaki a kusa da kayan zaben
- A martaninsa kan wannan zargi kakakin majalisar dokokin jihar ya ce jam’iyyar adawa ta shahara da yada labaran karya
Jam’iyyar SDP, a jihar Kogi, ta bukaci da a gaggauta mayar da kayayyakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Masu motsi zuwa Abuja, Daily Post ta rahoto.
Daraktan Sabbin Kafafen Yada Labarai, kwamitin Yakin Neman zabe Muri/Sam, Isaiah Davies Ijele, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya yi zargin cewa akwai shirin da wasu magoya bayan wata jam’iyya ke yi na mamaye dakunan da aka ajiye muhimman kayayyakin zabe Masu motsi dake Lokoja, jihar Kogi, domin lalata kayayyakin zaben.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Kotun Daukaka Kara ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Aliyu
Ya yi zargin cewa wani makusancin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Mista Kobo Adamu, wanda ake zargin ma’aikacin INEC ne ke da damar sanin duk wani bayani da ya shafi motsi da kuma ajiyar muhimman kayayyakin zaben.
“A matsayinta na cibiya mai zaman kanta, ba abin yarda ba ne a samu wasu mutane masu alaka ta kut-da-kut da manyan masu ruwa da tsaki, a kusa da kayan zabe, don haka muna bukatar shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya ba da umarnin a kai duk wani kayan aikin zabe Masu motsi cikin gaggawa zuwa ga babban ofishin Hukumar dake Abuja don kiyayewa.
“Bugu da kari kuma, ya kamata a baiwa duk wanda ke da kusanci da kayan aikin don kare dimokuradiyya a jihar Kogi.
Ya kara da cewa, “Ba za a iya yin illa ga lafiyar wadannan kayan zabe masu muhimmanci ba, musamman idan aka yi la’akari da dimbin kudaden gwamnati da masu biyan haraji da aka yi amfani da su wajen siyan su,” in ji shi.
Ijele ya hori INEC da gwamnatin tarayya da su gaggauta daukar matakin dakile duk wani yunkuri na bata martabar hukumar a jihar Kogi.
Da yake mayar da martani kan wannan zargi, babban sakataren yada labarai na kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Muhammed Yabagi ya ce jam’iyyar adawa ta shahara da yada labaran karya.
Ya ce, “Ba shakka wannan shi ne kukan ƙarshe na doki da ke mutuwa. Suna ci gaba da yada farfagandar da suke yadawa bayan da al’ummar jihar suka ki amincewa da su gaba daya da suka je yakin neman zabe wanda ya kama jihar baki daya maimakon wata manufa ta kabilanci kamar yadda jam’iyyar SDP da dan takararta, Muritala Yakubu Ajaka suka yi ta yadawa.”
A wani labarin kuma, Dimokuradiyyar Kasashen Turai Ba Ta Yi Kasa a Gwiwa Ba a Najeriya — Tsohon Minista ga Obasanjo
Tsohon Ministan Filaye, Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce abin da ake yi a Najeriya tun shekarar 1999 ba tsarin shugaban kasa ne na dimokuradiyyar Kasashen Yammacin Duniya ba
Kada mu zargi dimokuradiyyar Kasashen Turai, mu zargi kanmu da bullo da namu tsarin dimokuradiyya tare da gyare-gyare marasa iyaka
Mun gaji tsarin majalisar ne daga hannun Turawan mulkin mallaka kuma wannan tsarin mulkin dimokuradiyya ne inda shugabannin gwamnati ke samun halarcacciyar dimokuradiyya
Tsohon Ministan Filaye, Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce abin da ake yi a Najeriya tun shekarar 1999 ba tsarin shugaban kasa ne na dimokuradiyyar Kasashen Yammacin Duniya ba, amma tsarin dimokuradiyya ne da masu gudanar da tsarin suka gyara.
Ya kara da cewa tsarin dimokuradiyya irin na shugaban kasa bai yi kasa a gwiwa ba a Najeriya, inda ya ce ba a yi shi kamar yadda doka ta tanada ba.