- Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta tsige kakakin majalisar dokokin Nasarawa Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi da ga mukaminsa
- Tuni Alkalin kotun ya bayyana dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben
- Wannan Hukuncin dai tuni ya girgiza Kakakin Majalisar Dokokin da Kotun ta tsige
Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta tsige kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi da ga mukaminsa.
Kakakin Majalisar Dokokin dai ya kasance dan jam’iyyar APC Wanda ya Tsaya takara a cikinta.
KARANTA WANNAN: Mahaifiyar Dan Dabar da Ake Nema Ruwa Ajallo ta Mika Danta Ga ‘Yan Sanda
A hukuncin da ta yanke a ranar Talata, kotun ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Hon. Sa’ad Abdullahi Ibrahim (Turakin-Opanda), a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben mazabar Umaisha/Ugya ta jihar.
A wani labarin kuma, ‘Yan Boko Haram da Iyalansu 160k Sun Mika Wuya — Gwamna Zulum
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa kimanin mayakan Boko Haram guda dubu 160,000 da iyalansu sun mika wuya
Mika wuyan nasu ya samo asali ne sakamakon namijin kokarin da sojojin Najeriya suka yi akan su
Gwamnan ya nemi goyon bayan sojoji ta fuskar bunkasa ma’aikata domin baiwa jihar damar dakile yaduwar kananan makamai
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa kimanin mayakan Boko Haram guda dubu 160,000 da iyalansu sun mika wuya.
A cewarsa, mika wuyan nasu ya samo asali ne sakamakon rashin kishin kasa da sojojin Najeriya suka yi akan su.