- Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa yin amfani da yawan al’umma da albarkatun kasa zai samar da cikakken karfin tattalin arzikin tiriliyoyi na dala
- “Ajandar sabunta fata na gwamnatina ta fito ne da jajircewarmu na ganin mun samar da cikakken karfin tattalin arzikin kasarmu,inji Shugaba Tinubu
- Shugaban yace yayi alkawarina cewa ya himmatu wajen samar da yanayi mai dacewa ga kowace manufa, doka da aiki da ake bukata don ciyar da Najeriya gaba
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa yin amfani da yawan al’umma da albarkatun kasa, tare da mayar da hankali kan samar da cikakken karfin tattalin arzikin Nijeriya na ajandar Sabunta fata na gwamnatinsa na iya gina tattalin arzikin tiriliyoyi na dala nan da shekaru goma masu zuwa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin bude taron Injiniyoyi na 2023, Baje koli da Babban Taron Kungiyar Injiniyoyi na Kasa (NSE).
KARANTA WANNAN: Kotun Daukaka Kara ta Tabbatar da Kefas Agbu a Matsayin Gwamnan Taraba
Shugaban ya yi nuni da cewa, ana iya kara samun saukin hakan ta hanyar ci gaba da kokarin samar da ayyukan yi, samar da jari ga kanana da manyan ‘yan kasuwa, hada kai, bin doka da oda da yaki da yunwa, fatara da cin hanci da rashawa.
Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya ci gaba da cewa, da yawan al’umma da albarkatunta, Nijeriya za ta iya zama tattalin arzikin da ya kai tiriliyoyi na dala nan da shekaru goma masu zuwa.
Sai dai ya nuna rashin imani cewa za a iya cimma burin da aka sa gaba ba tare da la’akari da muhimmancin abubuwan da ke kunshe a cikin taken taron NSE, “Manufacturing, Competitiveness and Economic Growth.”
Shugaban ya ci gaba da cewa: “Ajandar sabunta fata na gwamnatina ta fito ne da jajircewarmu na ganin mun samar da cikakken karfin tattalin arzikin kasarmu, ta hanyar mai da hankali kan samar da ayyukan yi, samar da jari ga kanana da manyan ‘yan kasuwa, hada kai, bin doka da oda, da yaki da rashawa. yaki da yunwa da fatara.”
Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Stanley Nkwoch ya fitar, ta ce Tinubu ya dora wa NSE aiki kafada da kafada da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin “Hade hanyar da za a bi domin samun ci gaba mai dorewa ga Najeriya.”
Haka kuma shugaban ya kara da cewa:“Gwamnatinmu na bukatar goyon bayan ku don yin amfani da dimbin damammaki da ke gabanmu, da kuma mayar da alkawarin sabunta bege zuwa gaskiya ga daukacin al’ummarmu.
“Na sake yi muku alkawarina cewa na himmatu wajen samar da yanayi mai dacewa ga kowace manufa, doka da aiki da ake bukata don faruwar hakan.
“Ina ba ku kwarin gwiwa da ku shiga tattaunawa ta gaskiya, kuma ku fito tare da cikakken taswirar hanya da ke bayyana yadda, a matsayinmu na kasa, za mu iya amfani da masana’antu, fasaha da kirkire-kirkire a matsayin masu ingiza cim ma ajandar sabunta fata na takwas (8) na wannan Gwamnati. ”
“A matsayinmu na shugabannin da kuma kamfanoni masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki, mu auna nasarorin da muka samu ba wai ta hanyar ribar da muke samu ga masu hannu da shuni da masu hannun jari ba, har ma da yawan ‘yan Nijeriya da aka fitar daga kangin talauci, da yawan ayyukan yi da aka samar, da kuma tasirin ayyukan da muke yi a kai na yaki da cin hanci da rashawa,” ya kara da cewa.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayya ta Saki Fursunoni 37 Daga Gidan Yari
Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar harkokin cikin gida a Ranar Talata ta saki fursunoni 37 daga cibiyar gidan yari mafi girma ta Fatakwal
Sakin Fursunonin na daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka na rage cunkoso a gidajen yari
Tuni Gwamnati Tarayya gwangwaje Fursunonin da suka samun ‘yanci da tallafin Naira 10,000 domin saukaka komawa gida
Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar harkokin cikin gida a Ranar Talata ta saki fursunoni 37 daga cibiyar gidan yari mafi girma ta Fatakwal da kuma cibiyar gidan gyaran Hali da tarbiyya da ke Ahoada a jihar Ribas.
Dr Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da bikin sakin fursunonin a cibiyar gidan gyaran Hali da tarbiyya mafi girma ta Fatakwal.