- Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Kefas Agbu a matsayin gwamnan jihar Taraba
- Abaya dai Alkalin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ya yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP da dan takararta na gwamna suka shigar saboda rashin cancanta
- Hukuncin dai Bai Yiwa jam’iyyar data rashin Nasara a Kotun dadi ba
Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Talata ta tabbatar da zaben Kefas Agbu a matsayin gwamnan jihar Taraba.
A wani hukunci da aka yanke na bai daya da kwamitin mutane uku na kotun da mai shari’a Peter Afen ya zartar, kotun daukaka kara ta bayyana cewa jam’iyyar NNPP da dan takararta na gwamna, Farfesa Yahaya Sani, wadanda su ne masu shigar da kara. ba daidai ba ne a karar da suka shigar na adawa da zaben gwamnan da aka yi a ranar 28 ga watan Maris.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta Saki Fursunoni 37 Daga Gidan Yari
Mai shari’a Afen ya ce yayin da jam’iyyar NNPP da Sani suka yi roko ya soke zaben bisa dalilan rashin bin dokar zabe, sun kuma bukaci kotun da ta bayyana su a matsayin wadanda suka yi nasara a zabe daya bisa hujjar samun rinjayen kuri’u na halal.
Kotun ta ce ya sabawa doka ga duk wani mai kara kamar yadda ya faru a jam’iyyar NNPP da dan takararta na gwamna, su rika hura zafi da sanyi a lokaci guda.
Ya ci gaba da cewa, bayan da ya yi rokon a soke zaben saboda rashin bin dokar zabe, madadin rokon da a ce su ne suka lashe zabe da ba su da kafafun tsayawa.
Baya ga haka, Kotun daukaka kara ta ce bayanan karar da wadanda suka shigar da kara suka mika wa kotun bai cika ba, wanda hakan ya sa daukaka karar ta su ta gaza.
A saboda haka ne Mai shari’a Affen ya yi watsi da karar da aka shigar kan rashin cancanta sannan ya amince da hukuncin wata kotun da ta yi watsi da karar.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa a ranar 30 ga watan Satumba ne kwamitin alkalai guda uku karkashin jagorancin mai shari’a Ayo Sunmonu na kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Taraba ya yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP da dan takararta na gwamna suka shigar saboda rashin cancanta.
A wani labarin kuma, Kotun Daukaka Kara ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa
Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta tsige kakakin majalisar dokokin Nasarawa Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi da ga mukaminsa
Tuni Alkalin kotun ya bayyana dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben
Wannan Hukuncin dai tuni ya girgiza Kakakin Majalisar Dokokin da Kotun ta tsige
Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta tsige kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi da ga mukaminsa.
Kakakin Majalisar Dokokin dai ya kasance dan jam’iyyar APC Wanda ya Tsaya takara a cikinta.