- Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa harabar majalisar dattawa domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2024
- Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC a ranar Litinin ta amince da kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan N27.5
- An dai hango shugaban a harabar Majalissar cikin tsauraran matakan tsaro
Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa harabar majalisar dattawa domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2024.
An hango shugaban a harabar Majalissar da misalin karfe 11:04 na safiyar Laraba cikin tsauraran matakan tsaro.
KARANTA WANNAN: Nasarawa: Sojoji Sun Mayar da Martani Kan Harin da Masu Zanga-Zangar Suka Kai Wa Jami’ansu
Ku tuna cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC a ranar Litinin ta amince da kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan N27.5tn.
A wani labarin kuma, Za mu Iya Gina Tattalin Arzikin Tiriliyoyi na Dala da Al’ummarmu – Shugaba Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa yin amfani da yawan al’umma da albarkatun kasa zai samar da cikakken karfin tattalin arzikin tiriliyoyi na dala
“Ajandar sabunta fata na gwamnatina ta fito ne da jajircewarmu na ganin mun samar da cikakken karfin tattalin arzikin kasarmu,inji Shugaba Tinubu
Shugaban yace yayi alkawarina cewa ya himmatu wajen samar da yanayi mai dacewa ga kowace manufa, doka da aiki da ake bukata don ciyar da Najeriya gaba
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa yin amfani da yawan al’umma da albarkatun kasa, tare da mayar da hankali kan samar da cikakken karfin tattalin arzikin Nijeriya na ajandar Sabunta fata na gwamnatinsa na iya gina tattalin arzikin tiriliyoyi na dala nan da shekaru goma masu zuwa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin bude taron Injiniyoyi na 2023, Baje koli da Babban Taron Kungiyar Injiniyoyi na Kasa (NSE).