- Jami’an tsaro sun dakile tarzoma da zubar da jini a yayin da ‘yan daba da ‘yan bangar magoya bayan wata jam’iyyar siyasa a jihar Kogi suka mamaye hedikwatar INEC
- Sai dai tuni jami’an tsaro ciki har da jami’an ‘yan sandan Najeriya Suka dukufa domin dakile lamarin
- ‘Yan barandar siyasar sun tubure cewa ba za su iya barin alkalan zabe su kwashe kayan zaben zuwa kotun ba
Jami’an tsaro sun dakile tarzoma da zubar da jini a yayin da ‘yan daba da ‘yan bangar magoya bayan wata jam’iyyar siyasa a jihar Kogi suka mamaye hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da safiyar Laraba a Lokoja.
Mambobin jam’iyyun siyasar jihar sun hallara a hedikwatar INEC domin duba kayan zaben kamar yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta bayar a Lokoja, babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Gabatar da Kasafin Kudin 2024 Cikin Tsauraran Tsaro
Sai dai taron ya rikide zuwa tashin hankali a lokacin da wasu magoya bayan jam’iyyar suka yi gangamin yin awon gaba da harkar ta hanyar rera wakokin yaki da kuma barazanar kona ofishin INEC da kuma mayar da jihar ba za ta iya mulki ba.
‘Yan barandar da a bayyane suke yin amfani da miyagun kwayoyi suna ta kururuwa cewa ba za su iya barin alkalan zabe su kwashe kayan zaben zuwa kotun ba saboda jam’iyya mai mulki ta APC ta yi musu katsalandan.
Sai dai tuni jami’an tsaro ciki har da jami’an ‘yan sandan Najeriya Suka dukufa domin dakile lamarin.
LEADERSHIP, ta tattaro cewa tun da farko ‘yan bangar siyasar sun tare hanyar Post Office da titin Marine a karshen kofar shiga ofishin INEC kafin jami’an tsaro dauke da makamai su zo bude hanyoyin.
A wani labarin kuma, Nasarawa: Sojoji Sun Mayar da Martani Kan Harin da Masu Zanga-Zangar Suka Kai Wa Jami’ansu
Rundunar sojin Najeriya ta yi kakkausar suka kan abin da ta bayyana a matsayin wani harin ba-zata da aka kai kan sojoji da motocin sintiri a wata zanga-zanga
“Abin takaici, wannan rukunin masu zanga-zangar da suka kai hari kan motocin sintiri da ke dauke da sojoji a kan aikinsu
Sojojin Najeriya sun amince da mutunta ‘yancin ‘yan kasa na bayyana kokensu ta hanyar zanga-zangar lumana amma Yana kyau a jaddada cewa dole ne a gudanar da irin wannan zanga-zangar a cikin iyakokin doka
Rundunar sojin Najeriya ta yi kakkausar suka kan abin da ta bayyana a matsayin wani harin ba-zata da aka kai kan sojoji da motocin sintiri a wata zanga-zangar baya-bayan nan da ta faru a hanyar Lafia zuwa Makurdi a jihar Nasarawa.
An ce masu zanga-zangar sun tare babbar hanyar ne a matsayin martani ga sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamna a jihar.