- Majalisar zartaswar Adamawa ta amince da sake gina wani titi mai tsawon kilomita 44 Daya hada Wasu al’ummomi da dama
- Gwamnan ya amince da sama da Naira miliyan 117 a matsayin kwangilar gina dakin gwaje-gwaje na zamani a Asibitin kwararru
- Ana sa ran kammala aikin cikin watanni 12 masu zuwa
Majalisar zartaswar jihar Adamawa ta amince da sake gina wani titi mai tsawon kilomita 44 daga sansanin horar da masu yi wa kasa hidima na NYSC a Damare, kusa da babban birnin jihar, Yola, zuwa Borong, wata babbar al’umma a karamar hukumar Demsa.
Titin Feeder wanda ya ratsa ta kananan hukumomi biyu: Girei da Demsa, za a sake gina shi akan tsabar kudi Naira miliyan 836.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Bauchi ta Zabi Sabon Shugaba
Kwamishinan ilimi na jihar Dr Umar Pella ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar, SEC, wanda aka gudanar ranar Laraba a gidan gwamnati dake Yola.
Pella ya ce aikin wanda aka baiwa kamfanin Hydro Source and Resource Nigeria Limited, ana sa ran kammala shi cikin watanni 12 masu zuwa.
Taron na SEC na ranar Laraba wanda Gwamna Ahmadu Fintiri ya jagoranta ya kuma amince da sama da Naira miliyan 117 a matsayin kwangilar gina dakin gwaje-gwaje na zamani a Asibitin kwararru, Yola.
Pella wanda ya ce an fara bayar da aikin ne a kan sama da Naira miliyan 578, ya kuma bayyana cewa, an ba da kyautar ne domin kara farashin kayayyakin gini.
A wani labarin kuma, Gasar Zakarun Turai: Dan Wasa Erling Haaland Ya Kafa Sabon Tarihi a Duniyar Kwallo
Dan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaland ya kafa sabon tarihi na gasar zakarun Turai bayan ya ci kwallo a wasan da kungiyarsa ta doke RB Leipzig da ci 3-2
Tuni dai Haaland ya karya tarihin Kylian Mbappe na zamani
Haaland ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci kwallaye 40 a gasar zakarun Turai
Dan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaland, a ranar Talata ya kafa sabon tarihi na gasar zakarun Turai bayan ya ci kwallo a wasan da kungiyarsa ta doke RB Leipzig da ci 3-2.
Kwallon da Haaland ya zura a ragar RB Leipzig ita ce ta 40 a gasar zakarun Turai.