Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP, Kayode Egbetokun, ya ce ya samu amincewar shugaba Bola Tinubu kan daukar ‘yan sanda 30,000 a duk shekara.
Egbetokun ya bayyana haka ne a wata ziyarar aiki da ya kai jihar Adamawa ranar Talata,inda ya bayyana cewar gwamnatin ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Karanta nanMajalisar Dokokin Bauchi ta Zabi Sabon Shugaba
Ta amince da daukar ‘yan sanda 10,000 a duk shekara. Sabuwar amincewar za ta ninka adadin ‘yan sandan da ake dauka a kasar sau uku a kowace shekara.
IGP ya bayyana cewa korafe-korafen da ake yi na cewa jami’an ‘yan sanda sun yi wa aiki fiye da kima zai zama tarihi da zarar an aiwatar da sabuwar amincewar.
Shugaban ‘yan sandan ya ce,na san kamar a yau a Najeriya, dan sanda daya yana aikin jami’ai biyu zuwa uku, na san yadda ake ta fama da nauyi.
Lokacin da muka shiga aikin ‘yan sanda, abin da muka hadu da shi shi ne aiki sau uku, safe, rana da dare. Amma kamar yadda shekaru ke tafiya, sai ya zama sau biyu, safe da dare. A wasu wurare ma kuna iya yin aiki na awanni 24.
Lokacin da nake kwamandan yanki a Osogbo, ina da ’yan sanda da suke aiki ba dare ba rana har tsawon mako guda, domin a lokacin da suke rufewa daga aikin safiya, suna ci gaba da aikin dare.
Kuma idan jama’a suka ga suna kwana a bainar jama’a, sai su rika yi musu bidiyo, suna yi musu ba’a,don haka ina sane da halin kuncin da kuke ciki sakamakon yawan fama da aikin yi.
Lokacin da na zama Sufeto Janar na ‘yan sanda, abu na farko da na yi shi ne na lura da batun ma’aikata. Gwamnatin Tarayya da ta gabata ta amince da daukar ’yan sanda 10,000 duk shekara.
A wani labarin kumaGwamnatin Adamawa ta Amince da N836m Don Sake Gina Titi
Amma da wannan sabuwar gwamnati, na samu amincewar shugaban kasa na daukar 30,000 na tsawon shekaru hudu masu zuwa,na san da zarar mun tabbatar da wannan amincewar, batun karancin ma’aikata zai zama tarihi.
Egbetokun ya kuma tabbatar wa da jami’an ‘yan sanda cewa nan ba da dadewa ba ‘yan sanda za su fara bayar da lambobin yabo ga jajirtattun jamiai yana mai cewa ta wannan hanya ne kawai kowa zai iya samun karin girma na musamman, a gaba.