- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tashi daga birnin Abuja na Najeriya zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa
- Shugaban Zai bi sahun sauran shugabannin Kasashen duniya don tattauna muhimman Bayanai
- Tinubu Zai Samu rakiyar manyan jami’ian Gwamnatin sa
Shugaban kasa, Bola Tinubu a Ranar Laraba ya tashi daga birnin Abuja na Najeriya zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ake sa ran zai halarci taron sauyin yanayi na COP28.
A yayin taron da aka shirya gudanarwa a ranakun 1 da 2 ga watan Disamba, 2023, Tinubu zai gabatar da jawabi da zai bayyana matsayin Najeriya kan batutuwa daban-daban da suka hada da makamashi mai sabuntawa da kuma samar da kudaden yanayi.
KARANTA WANNAN: JAMB ta Sanya Ranar Yin Rijistar Jarabawar UTME 2024
Wata sanarwa da mai baiwa Tinubu shawara ta musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata ta ce shugaban zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnati.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa shugaban kasar ya bar kasar ne sa’o’i kadan bayan gabatar da kasafin kudin shekara ta 2024 ga taron hadin gwiwa na majalisun dokokin kasar.
A wani labarin kuma, Sojojin Ruwan Najeriya Sun Mika Buhunan Tabar Wiwi 187 ga NDLEA
Rundunar Sojin ruwan Najeriya (NNS) BECROFT ta mika buhunan tabar wiwi 187 ga hukumar NDLEA a wani aikin hadin gwiwa tsakanin hukumomi
Yaki da miyagun laifuka da aikata laifuka a cikin ruwa ya kasance babban abin damuwa
Rundunar sojin ruwa za ta ci gaba da bibiyar masu aikata laifuka tare da hana miyagun kwayoyi shiga Najeriya
Sojin ruwan Najeriya (NNS) BECROFT ta mika buhunan tabar wiwi 187 ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a wani aikin hadin gwiwa tsakanin hukumomi.
Kwamandan rundunar, Commodore Kolawole Oguntuga, ya mika wa jami’an NDLEA kayayyakin da aka kama a NNS BEECROFT da ke Apapa, Legas.