- Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a, JAMB, ta bayyana ranar da za a gudanar da rijistar jarrabawar UTME 2024
- Dole ne Kowanne Dan takara ya ziyarci gidan yanar gizon hukumar don naman kowane bayani
- “An bukaci ‘yan takara da su lura da wadannan ranaku da sauran shawarwarin da hukumar ta bayar game da yadda ake gudanar da jarrabawar
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a, JAMB, ta bayyana ranar da za a gudanar da rijistar jarrabawar UTME 2024.
Hukumar, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba ta hannun mai ba ta shawara kan harkokin sadarwa, Fabian Benjamin, ta ce za a fara sayar da fom din ne daga ranar 15 ga watan Janairu zuwa 26 ga Fabrairu, 2024.
KARANTA WANNAN: Sojojin Ruwan Najeriya Sun Mika Buhunan Tabar Wiwi 187 ga NDLEA
Sanarwar ta bayyana cewa MOCK-UTME 2024 an tsara yinta a ranar 7 ga watan Maris, yayin da UTME “za ta gudana daga Ranar 19th zuwa 29 ga watan Afrilu, 2024”.
Ya kara da cewa “Ana sa ran ‘yan takara za su fitar da fom din jarrabawar su daga ranar 10 ga watan Afrilu, 2024.
“An bukaci ‘yan takara da su lura da wadannan ranaku da sauran shawarwarin da hukumar ta bayar game da yadda ake gudanar da jarrabawar. Dole ne su kuma ziyarci gidan yanar gizon hukumar @www.jambgov.ng don naman kowane bayani.”
A wani labarin kuma, Gwamnatin Adamawa ta Amince da N836m Don Sake Gina Titi
Majalisar zartaswar Adamawa ta amince da sake gina wani titi mai tsawon kilomita 44 Daya hada Wasu al’ummomi da dama
Gwamnan ya amince da sama da Naira miliyan 117 a matsayin kwangilar gina dakin gwaje-gwaje na zamani a Asibitin kwararru
Ana sa ran kammala aikin cikin watanni 12 masu zuwa
Majalisar zartaswar jihar Adamawa ta amince da sake gina wani titi mai tsawon kilomita 44 daga sansanin horar da masu yi wa kasa hidima na NYSC a Damare, kusa da babban birnin jihar, Yola, zuwa Borong, wata babbar al’umma a karamar hukumar Demsa.
Titin Feeder wanda ya ratsa ta kananan hukumomi biyu: Girei da Demsa, za a sake gina shi akan tsabar kudi Naira miliyan 836.