- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara gudanar da bincike kan harin da aka kai gidan kwamishinan zaben Kogi, Gabriel Longpet
- Batare da wani Bata lokaci ba jami’an ‘yan sandan da ke bakin aiki a gidan sun yi wa ‘yan bindigar ruwan wuta tare da hana su shiga harabar gidan
- Tuni Rundunar ‘yan Sanda ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa kwamishinan zaben Jihar Kogi
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara gudanar da bincike kan harin da aka kai gidan kwamishinan zabe na jihar Kogi, Gabriel Longpet, Daily Post ta rahoto.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya a wata sanarwa a ranar Juma’a ya ce kwamishinan ‘yan sandan Bethrand Onuoha ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa REC na Kogi.
KARANTA WANNAN: Sama da ‘Yan gudun Hijira 20k Daga Kasar Kamaru Sun Nemi Mafaka a Najeriya
Da yake bayyana abin da ya faru a wurin, Kakakin ‘yan sandan ya ce, “Rundunar ‘yan sandan ta samu damuwa a yau 1/12/2023 da misalin karfe 03:11 a kan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai wa ofishin hukumar zabe ta INEC, suka kuma fara harbe-harbe kai tsaye.
“Jami’an ‘yan sandan da ke bakin aiki a gidan sun yi wa ‘yan bindigar ruwan wuta tare da hana su shiga harabar gidan.
“A halin da ake ciki, an ga motar kirar Sienna da suka zo da ita ta kone kurmus a kofar gidan.
“Nan da nan, Kwamishinan ‘yan sandan ya tura da tawagar masu taimakawa wajen da abin ya faru yayin da suke bin maharan. Ya yabawa masu gadin da ke bakin aiki bisa jajircewa da kwazon su”.
Aya ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta jajirce wajen kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su gaban kuliya.
“Kwamishinan, yayin da yake tabbatar wa mutanen jihar Kogi nagartattun al’ummar jihar bisa jajircewarsu wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin duk ‘yan kasa, ya bukace su da su hada kai da Hukumomin tsaro ta hanyar ba da batanai masu sahihanci kan lokaci kan lamarin.
“Sanarwar ta kara da cewa Rundunar ta himmatu Domin dakile ayyukan masu aikata laifuka a jihar don ba da damar mayar da martani cikin gaggawa.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Jirgin NAF Yayi Hatsari
Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakin rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers
Jirgin ya yi hatsari ne jim kadan bayan ya tashi domin yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa
Tuni shugaban hafsan sojin saman Air Marshal Hasan Abubakar ya nufi wurin da lanarin ya afku domin ganin halin da ake ciki
Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakin rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a ranar Juma’a a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Edward Gabkwet, kakakin NAF, ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.