- A yayin da ake ta cece-kuce kan nadin kwamitocin riko da gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya yi, majalisar dokokin jihar ta tabbatar da sunayen wadanda aka nada
- Yin amfani da kwamitocin riko wajen maye gurbin zababbun shugabannin Kananan Hukumomi ya sabawa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999
- Majalisar dattawan ta bukaci gwamnan jihar Benue da ya sake duba rushen shugabannin Kananan Hukumomi tare da mayar da wadanda aka zaba
A yayin da ake ta cece-kuce kan nadin kwamitocin riko da gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya yi, majalisar dokokin jihar ta tabbatar da sunayen wadanda aka nada, Daily Post ta rahoto.
Wannan tabbaci na zuwa ne duk da kiran da Majalisar Dattawa ta yi ga Gwamnatin Tarayya ta hana nada shugabannin kananan hukumomin da ba za a yi zabe ta hanyar dimokradiyya a fadin kasar nan ba.
KARANTA WANNAN: Mataimakin Shugaban Majalisa, Kalu Ya Gargadi Matasa Game da Garkuwa da Mutane, Tayar da Zaune Tsaye
Kudurin Majalisar ya biyo bayan wani kudiri mai taken “Bukatar gaggawar Dakatar da Rugujewar Dimokuradiyya da Rushe Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Binuwai,” wanda Sanata Abba Moro ya dauki nauyi a zauren Majalisar ranar Juma’a.
Moro ya jaddada cewa yin amfani da kwamitocin riko wajen maye gurbin zababbun shugabannin Kananan Hukumomi ya sabawa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima).
Majalisar dattawan ta bukaci gwamnan jihar Benue da ya sake duba rushen shugabannin Kananan Hukumomi, da kundin tsarin mulkin kwamitocin riko, tare da mayar da wadanda aka zaba.
Sai dai a bijirewa wannan umarni majalisar dokokin jihar Binuwai ta tabbatar da mutum 21 daga cikin 23 da aka tantance.
Wadanda aka nada daga Oju da Obi sun sauka. Ana sa ran ƙarin sabuntawa game da wannan batu.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Bayan Zanga-Zangar Dalibai Jami’ar ATBU ta Rufe Harabarta
Hukumomin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Yelwa a jihar Bauchi sun rufe makarantar sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan da aka yi wa wani dalibi
Manufar Garkame Jami’ar shi ne hana tabarbarewar doka da oda yayin da ake zargin wasu ‘yan daba ne suka sace zanga-zangar
An umurci dukkan daliban makarantun biyu da su fice daga harabar jami’ar ba tare da bata lokaci ba, saboda rashin bin umarnin na iya haifar da hukuncin da ya dace daga hukumar
Hukumomin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Yelwa a jihar Bauchi sun rufe makarantar sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan da aka yi wa Joseph Agabaidu, dalibin sashen nazarin kasa na shekarar karshe, a wani yunkurin fashi da makami.
A cikin wata takarda da aka fitar wadda mataimakiyar rijistarar ta sanya wa hannu, Haj. Fatima Inuwa Abdullahi,tace hukumar gudanarwar jami’ar ta amince da rufe jami’ar na tsawon mako guda daga ranar Litinin 4 ga watan Disamba zuwa Lahadi 10 ga watan Disamba.