- Wasu mazauna gari sun ceto wata jaririya da aka yi watsi da ita a cikin magudanar ruwa da ke gefen titi a Jihar Adamawa
- Tuni dai aka sami wani mai tausayi wanda ya yiwa jaririyar wanka ya Sanya ta cikin tufafi
- Bai kamata kuyi ciki ba Idan ba za ku iya reno da kula da jaririn ba
Yanzu haka dai wasu mazauna gari sun ceto wata jaririya da aka yi watsi da ita a cikin magudanar ruwa da ke gefen titi a garin Yola na jihar Adamawa.
An gano jaririyar ne a gundumar Kofar Bayi da ke Yola da sanyin safiyar Laraba, 6 ga watan Disamba, 2023.
KARANTA WANNAN: Dalilan da Suka Sanya ‘Yan Najeriya Ba Su Amince da APC, PDP da Sauran Jam’iyyu Ba – Akpabio
Da samun jaririyar, wani mai tausayi ya yi mata wanka ya nade ta Cikin tufafi.
Shitu Abdulqadir Yola, wani mazaunin garin ne ya kai rahoto lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke kusa da wurin.
“Ina cikin barci ‘yan sa’o’i da suka gabata a safiyar yau, sai na ji kururuwa da hayaniya yayin da mutane suka shiga gidan danginmu da ke titin Shehu, cikin garin Yola. Sai naji Goggona tana fadin, ‘Subhanallah! Wane irin zalunci ne muke rayuwa a ciki,” in ji shi.
“An gano wata jaririya a cikin wani karamin magudanar ruwa da ke kusa da gidanmu. Aka dauko yarinyar aka shigo da ita gidanmu, inda kakarmu ta yi mata wanka.” Ya ci gaba da cewa.
“Da fitowa daga dakina, na ga taron mutane a harabar gidanmu. Na shawarce su da su adana jakar da aka tsinci yaron a cikinta sannan su gaggauta kai rahoton lamarin ga ofishin ’yan sanda da ke kusa, wanda a karshe suka yi hakan.
“Hoton da aka makala a kasan wallafar yana nuna jaririyar da aka yasar. Shin haka ne a kowace rana wasu mutane a cikin al’ummarmu ke zama marasa zuciya? Idan ba za ku iya reno da kula da jaririn ba, don me za ku kawo ta cikin duniya?
A wani labarin kuma,Wani Dan Wasan kwallo Ya Fadi Ya Mutu Ana Tsaka da Atisaye
Dan wasan kwallon kafa mai suna Sodiq Adebisi dan asalin jihar Ogun ya rasu bayan ya fadi yayin atisaye a filin wasa
Lokacin da abokan wasansa suka ga matashin ya fadi, tuni suka garzaya da shi asibitin jiha
Iyalin Marigayin sun ce ba sa son wani bincike kuma suna son a binne marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
Dan wasan kwallon kafa mai suna Sodiq Adebisi dan asalin jihar Ogun ya rasu ne bayan da ya fadi yayin atisaye a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.
Rahotanni sun ce dan wasan yana atisaye da wasu ‘yan wasan kwallon kafa a ranar Asabar lokacin da lamarin ya faru.