- Hukumar NPC ta gargadi jami’an da ke da ruwa da tsaki wajen tattara bayanan jama’a na shekarar 2023-2024
- NPC tace duk wani nau’i na magudi zai haifar da mummunan sakamako ga jami’an da kuma kasa baki daya
- Dole ku Baiwa Ayyukan ku muhimman ci lokacin da kuke Gudanar da Bincike
Hukumar Kidayar jama’a ta Kasa NPC ta gargadi jami’an da ke da ruwa da tsaki wajen tattara bayanai na shekarar 2023-2024, da su tabbatar da sahihancin bayanai daga wadanda suka amsa.
Mista Chidi Ezeoke, kwamishinan tarayya na NPC mai wakiltar jihar Anambra, shine Wanda ya yi wannan gargadin a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Awka.
KARANTA WANNAN: Najeriya Ta Fi Kashe Kudi Wajen Ciyar da Karnuka Fiye da Fursunoni a NCS – CG
Ezeoke, wanda Dr Joachim Ulasi, Daraktan NPC na jihar ya wakilta, ya ce duk wani nau’i na magudi zai haifar da mummunan sakamako ga jami’an da kuma kasa baki daya.
Sai dai ya ba da tabbacin cewa an yi wa jami’an da aka zaba gwaji kuma an amince da su kuma za su yi aikin da ya dace bayan an yi musu horo mai zurfi na tsawon makonni uku.
“Kada ku sarrafa bayanai kuma kada ku zauna a wuri kuyi hira da kanku saboda idan kun yi haka, zaku maimaita amsoshi iri ɗaya.
“Lokacin da za ku yi hira da mutane 20, tabbas ra’ayinsu ya bambanta. Sirrin binciken kenan.
‘Na yi imani da dokar Kama. Don haka duk wani nau’i na magudi zai shafi jami’in da kuma kasar nan gaba kadan,” inji shi.
Ezeoke ya ce binciken zai shafi kananan hukumomi 20 na jihar, ban da Ayamelum da aka gudanar da binciken mutane a cikin shekarar 2018.
Ya ce binciken zai gudana ne daga ranar 7 ga watan Disamba zuwa 21 ga watan Afrilu, 2024, a gungu 38 da ke cikin wadannan kananan hukumomi 38 da aka zaba.
Kwamishinan Tarayyar ya ce binciken zai taimaka wajen tsara manufofi masu tushe, inganta ayyukan kiwon lafiyar jama’a da kuma ba da gudummawa ga ajandar ci gaban jihar gaba daya.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayya Ta Saki Fursunoni 178 a Jihar Jigawa
Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 178 daga cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya da ke jihar Jigawa
Cunkoso a cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya ya na kawo cikas ga kokarin hukumar ta NCoS a shirye-shiryen yin gyara
Aa bukaci fursunonin da aka saka da su kasance masu halin kirki kuma su kasance jakadu nagari na zaman lafiya da tsaro
Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 178 daga cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya da ke jihar Jigawa ta hannun ma’aikatar harkokin cikin gida.
Kakakin Hukumar Kula da gidan yari na Najeriya a Jigawa, Muhammad Sani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Alhamis.