- ‘Yan sandan kasar Saliyo sun gayyaci tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma domin amsa tambayoyi a wani bangare na binciken abin da gwamnati ta kira yunkurin juyin mulki
- Wannan dai na zuwa Ne biyo bayan wasu mahara dauke da muggan makamai sun kai hari a wurare daban-daban
inda suka yi artabu da jami’an tsaro - A shirye nake in goyi bayan binciken ‘yan sanda gaba daya, a cewar tsohon Shugaban Kasar
‘Yan sandan kasar Saliyo a Ranar Alhamis sun gayyaci tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma domin amsa tambayoyi a wani bangare na binciken abin da gwamnati ta kira yunkurin juyin mulki a makon da ya gabata, in ji jami’ai.
An bukaci Koroma, wanda ya jagoranci kasar ta yammacin Afirka tsawon shekaru 11 har zuwa shekarar 2018, da ya gurfana a sashen binciken manyan laifuka da ke Freetown babban birnin kasar cikin sa’o’i 24, in ji ma’aikatar yada labaran kasar.
KARANTA WANNAN: Hukumar NPC ta Gargadi Jami’anta Game da Magudin Bayanai
Wasu mahara dauke da muggan makamai sun kai hari a wani rumbun ajiye makamai na sojoji da bariki biyu da gidajen yari biyu da ofisoshin ‘yan sanda biyu, inda suka yi artabu da jami’an tsaro a safiyar ranar 26 ga watan Nuwamba.
Fadan dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a cewar ministan yada labaran kasar Chernor Bah. Tun daga wannan lokacin, an kama mutane 71.
Sanarwar da ma’aikatar yada labaran kasar ta fitar ta ce “An gayyaci tsohon shugaban kasar ne da ya taimaka a binciken da ake yi na aikata laifuka kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 26 ga watan Nuwamba a Saliyo.
Ofishin tsohon shugaban kasar ya mayar da martani a wata sanarwa ta daban a ranar Alhamis cewa zai je Freetown domin bayar da hadin kai ga binciken.
Mukarrabansa sun ce yana garin Makeni ne a arewacin kasar.
“Ina mai da hankali sosai kuma a shirye nake in goyi bayan binciken ‘yan sanda gaba daya,” in ji Koroma a cikin sanarwar.
“Bari mu bi doka da oda a mulkin demokradiyyarmu.”
Ya yi kira da a kwantar da hankula sannan ya bukaci mabiyansa da su taimaka wa ‘yan sanda a binciken da suke yi.
Hukumomin kasar sun ce ana zargin tsaffin masu gadin Koroma da hannu a cikin lamarin na ranar 26 ga watan Nuwamba.
Yammacin Afirka dai na fama da jerin juyin mulki tun shekarar 2020 inda sojoji suka karbe mulki a Mali, Burkina Faso, Nijar da Guinea.
A ranar Asabar din da ta gabata ne shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya yi ikirarin cewa ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin juyin mulki bayan an gwabza tsakanin sojoji da wasu sassan jami’an tsaro. AFP
A wani labarin kuma, Najeriya Ta Fi Kashe Kudi Wajen Ciyar da Karnuka Fiye da Fursunoni a NCS – CG
Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya ta bayyana cewa ta fi kashe kudade wajen ciyar da karnuka fiye da ciyar da fursunoni
Abun mamaki dan Najeriya da ba a yanke masa hukunci ba, ana ciyar da shi Naira 750, ya yin da ake ciyar da kowane kare ka Naira 800 a kowace rana
Wannan na zuwa Ne Yayin da Gwamnatin Tarayya take kokarin Sakin Fursunoni Daga gidajen yari daban-daban Dan rage cunkoso
Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya ta bayyana cewa ta fi kashe kudade wajen ciyar da karnuka fiye da ciyar da fursunoni da kuma gyara wadanda suka yi zaman gidan yari.
Kwanturolan hukumar ta NCS, Haliru Nababa ya bayyana haka a wajen kare kasafin kudin 2024 lokacin da ya gurfana gaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin cikin gida a majalisar tarayya Abuja.